Daga Ibrahim Muhammad
jigo a tsarin tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano daga yakin ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Muhammad Adamu da aka fi sani da Bomboy ya bayyana cewa a matsayinsu na ‘yan ƙaramar hukumar da suke tare da ɗan majalisarsu na tarayya mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa, suna godiya ga Allah da jagoran Kwankwasiyya na ƙasa Daka Rabi’u Musa Kwankwaso a kan tsayar musu da Hon. Hasan Shehu Husaini da aka yi suka zaɓe shi a matsayin wakilinsu a Majalisar Tarayya.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a kan irin wakilci da ɗan majalisar yake ya ce domin tun zuwan sa Majalisar Tarayya ya zo da ƙudurce-ƙudurce da suka shafi bunƙasa cigaban al’ummar yankin, idan aka yi duba da ɓangaren harkar ilimi da shi ne ƙashin bayan tafiyar Madugunsu na Kwankwasiyya da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ya yi abubuwa da yawa da bunƙasa fannin lafiya da kyautata zamantakewa da ayyukan bunƙasa rayuwa.
Hon. Muhammad Adamu Bomboy ya yi nuni da cewa daga ƙudurce-ƙudurce da Ɗan Majalisar nasu Hon. Hassan Shehu Husaini ya kawo a zuwan sa Majalisa cikin kusan shekaru bIyu yana mutuƙar yin hidima a kan abin da ya shafi cigaban al’ummar jihar Kano gaba ɗaya.
Ya ce irin ayyuka da ya yi sun hada da na haɓɓaka asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da sama musu Cibiya ta kula da ciwon zuciya, sannan ya kai ƙudiri na haɓɓaka ɓangaren masana’antu a jihar Kano.
Bombay ya ƙara da cewa a irin koyi da yake da shi na tsarin tafiyarsu ta Kwankwasiyya yana bai wa ilimi kulawa sosai, ya ɗauki nauyin karatun yara ƙanana marasa gata tun daga makarantar reno har Firamare har gaba, ya kuma ɗauki nauyin jarabawar ɗalibai tun daga NECO da WEAC da JAMB.
Ya ƙara da cewa sannan yana ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a manyan makarantu daban-daban a ciki da wajen Kano da gina ajujuwa da asibitoci da gudanar da tituna a mazaɓu da dama da sanya fitilun masu hasken rana da sama wa matasa ayyukan yi da tallafa wa matasa da jari, yana tallafawa mutane da dama da ababen hawa, musamman ‘yan siyasa da sauran al’umma a fannoni da dama.
Hon. Muhammad Adamu Bomboy ya ƙara da jaddada godiya ga Allah da ya ba su Wakili jajiirtacce mai aiki tuƙuru da a cikin shekaru biyu ya bijiro da ayyukan da har sai da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya zo ƙaddamar da wasu daga ayyukansa ya yaba masa ya nemi sauran ‘yan majalisa su yi koyi da shi.








