Daga Ibrahim Muhammad
An rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar ‘yan jarida na yanar gizo reshen jihar Kano.
Taron an gudanar da shi ne a sakatariyar ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen jihar Kano.
Shugaban kwamitin ƙaddamar da ƙungiyar, Alhaji Ahmad Aminu, ya buƙaci ‘yan jarida na yanar gizo su riƙa tantance gaskiyar labarai kafin wallafawa domin kauce wa yaɗa labaran ƙarya da kan iya haifar da rikici.
Sabon shugaban ƙungiyar, Kwamared Abubakar Ɗangambo, ya bayyana ƙudurinsa na haɗa kai da sauran ‘yan ƙungiyar domin kare martabar aikin jarida da kuma tallafawa cigaban jihar Kano.
Ya ce za su yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da sahihancin bayanai da wayar da kan al’umma cikin gaskiya da riƙon amana.
Sauran sabbin shugabannin da aka rantsar sun haɗa da Khadijah Aminu a matsayin mataimakiyar Shugaba, Isyaku Ahmad a matsayin Sakatare. Zahara’u Nasir a matsayin mataimakiyar sakatariya, Abbas Yusha’u a matsayin Ma’ajin Kuɗi, da Zainab Bello a matsayin mataimakiyar Ma’aji.
Taron rantsarwar ya samu halartar ‘yan jarida da dama daga faɗin jihar Kano.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya Abubakar Abdulkadir Ɗangambo murna bisa zabensa da aka yi a matsayin Shugaban ƙungiyar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce kafa wannan sabon reshe na kafafen yaɗa labarai ta yanar gizo, ƙarƙashin ƙungiyar ‘yan jarida na jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Kwamared Sulaiman Dederi, zai taka rawa wajen tallafa wa kafafen yaɗa labarai wajen tabbatar da gaskiya da adalci a rahotanni.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da goyon bayan duk wani ƙoƙari da zai inganta harkar yaɗa labarai da kuma ƙarfafa haɗin kan ‘yan jarida domin ci gaban jihar Kano.






