Al’ummar Zango Sun Karrama Dakta Muhammad Musa Bayan Kammala Aiki A NNPC

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar ci gaban al’ummar Zango (Zango Community Development Association) da haɗin gwiwar Gidauniyar Fatah Zango (Fatah Zango Foundation) da ke ƙaramar hukumar Birnin Kano, sun gudanar da taron karrama Dakta Muhammad Musa Zango, tsohon manajan daraktan ayyukan kula da lafiya na kamfanin NNPC.

Taron an gunadar da shi ne a rufafffen ɗakin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a ranar Asabar da ya sami halartar ɗimbin mutane daga ciki da wajen jihar Kano da suka ƙunshi iyaye da iyalansa da ‘yan’uwa da sauran abokan arziƙi da abokan aikinsa.

A jawabinsa na maraba, shugaban taron, Ambasada Rabi’u Ɗan Sittta ya bayyana cewa taron an shirya shi ne domin karrama Dakta Musa Zango bisa la’akari da irin gudunmuwa da yake bayarwa ga ci gaban al’umma.

Shi ma wanda aka yi taron domin karrama shi, Dakta Muhammad Musa Zango ya nuna matuƙar farin cikinsa da gode wa Allah da mutanen unguwannin Zango da na Ƙofar Mata da na Zage da suka zo don karrama shi da shugabanninsu.

Ya ƙara da cewa shi wasu abubuwa da ake faɗa yana yi wa al’umma ba ya iya tuna su, amma akwai abubuwa da yawa bai ma san abin da ake ba ana yi ne don Allah, don dai an kira shi ne a taron ya zo ya ji ana faɗa, kuma abubuwa suna nan ana yi a ƙarƙashin Gidauniyar Zango Fatah da mutane su za su faɗa.

Ya ƙara da cewa ba za su tsaya ba, za su ci gaba da ba da gudunmuwa ta haɗa kai da ƙarfinsu wajen tallafawa cigaba da bunƙasa rayuwar al’umma.

Ya ce kullum yana jan hankalin yara ƙanana da matasa da suke tare da ba su shawara a kan su kama ilimi da tarbiyya da bin iyaye domin suna taimakawa wajen cimma nasara a rayuwa, domin idan ba don wannan ba su ma da ba za su kai labarai ba.

Dakta Muhammad Musa Zango ya ce kada matasa su yi wasa da wannan, domin idan suka jajirce duk wahala idan aka dage aka yi karatu aka bi ƙa’ida da Allah ya yi umurni aka bi iyaye da yardar Allah za a ga alheri wanda su ma shi suke nema wa mutane, ba wani abu da suke nema sai alheri da kuma son cigaban al’umma da zaman lafiya a tsakaninsu.

Hon. Shu’aibu Idris Zango, shugaban kwamitin da ya shirya taron da aka karrama Dakta Muhammad Musa, ya ce sun karrama shi ne domin su nuna wa duniya wannan ɗa nasu suna alfahari da shi da amfanar sa su da ‘yan’uwansu da ‘ya’yansu da iyayensu, suna kuma sa ran cigaba da amfanar sa shi ya sa suka ce abin da yake suka ga cancantar su fito su karrama shi a mahaifarsa.

Ya yi nuni da cewa a Zango aka haifi Dakta Muhammad, nan ya girma ya yi wayo, kuma sun faɗi irin alherai da yake aiwatarwa a gaban jama’a, abin da suka faɗa idan akwai abin da ba haka ba ne wani zai ce ba gaskiya ba ne, amma duk al’umma da suka halarci taron shaida ne an faɗi irin abubuwa da ya yi na alherai kowa ya yi shiru sun tabbatar ana yi ke nan.

Shu’aibu Zango ya ƙara da cewa zai iya tunawa Dakta Muhammad Musa Zango sama da shekaru 18 in ka je masa da buƙata tsakani kai da shi ka tambaye ya ba ka idan ma ba ka tambaya ya taimake ka. “Da mabuƙatun al’umma suka yi yawa sai ya ƙirƙiri Gidauniya Fatah Zango yana zuba kuɗi ana tallafa wa mutane ta fannoni da dama,” in ji shi.

Hon. Shu’aibu Idris Zango ya ce a wannan taron da suka gudanar sun karrama Dakta Muhammad Musa, gobe ma za su duba wani da yake da kishi da ba da gudunmuwa ga al’umma shi ma su karrama shi.

Shugaban kwamitin gudanar da taron, ya kare ƙorafin da ake na cewa an gudanar da taron da Turanci maimakon da Hausa, inda matane da dama suke nuna rashin jin daɗin haka bayan kashi 99 na mahalarta Hausawa ne.

Ya ce sun yi da Turanci ne saboda suna so duniya ta sani duba da inda Dakta Musa ya yi aikin ya gama a NNPC ƙabilu ne kala daban-daban, sannan akwai abokansa na waje da ba sa jin Hausa da suka bibiyi taron kai tsaye ta kafofin sadarwa.

A yayin taron an ƙaddamar da kalanda da ta ƙunshi hotunan shugabannin Gidauniyar Zango Fata da na ƙungiyar cigaban al’ummar Zango.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara