An Naɗa Ɗan Amana Sarautar Magajin Garin Kasuwar Ƙofar Wambai, Kano

Daga Imam Muhammad

Sarkin kasuwar Ƙofar Wanbai, Alhaji Bashir Adamu ya naɗa Alhaji Ibrahim Lawan Ɗan Amana, sarautar Magajin Garin Kasuwar Ƙofar Wanbai.

Taron naɗin wanda ya gudana a ƙarƙashin jagorancin majalisar Sarkin Kasuwar Ƙofar Wambai ranar Laraba, ya sami halartar ‘yan kasuwa daban-daban.

A jawabinsa ga manema labarai bayan naɗa shi magajin garin kasuwar Ƙofar Wambai, Alhaji Ibrahim Ɗan Amana ya yi godiya ga masarautar Kano ƙarƙashin Khalifa Muhammad Sanusi da wakilin Gabas da Sarkin Kasuwar Ƙofar Wambai bisa wannan sarauta da suka sahale aka yi masa naɗin.

Ya nuna gamsuwa da irin ayyukan da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf yake na cigaban al’ummar Kano kuma za su yi amfani da wannan naɗin da aka yi masa wajen cigaba da tallafawa bunƙasa haɗin kai da cigaban ‘yan kasuwar Ƙofar Wambai.

Alhaji Ibrahim Lawan Ayagi Ɗan Amana ya gode wa dimbin ‘yan kasuwa da ƙungiyoyi daban-daban da sauran mutane da suka nuna masa ƙauna suka zo suka shaidi naɗin nasa da kuma taya shi murna.

Shi ma shugaban gamayyar ƙungiyoyin kasuwar Ƙofar Wambai gaba ɗaya wanda kuma shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ‘yan koli na kasuwar, kuma ɗan majalisar masarautar Sarkin kasuwar Ƙofar Wambai, Alhaji Shariff Nata’ala Isma’il, ya ce ba su yi mamakin naɗin da aka yi wa Ibrahim Ɗan Amana sarautar ba.

Ya ce ganin irin tsare-tsaren da masarautar take da shi na wakilai da suke kula da dukkan wasu al’umma da suke a cikin kasuwar tasa aka yi wannan naɗin wanda ƙoƙari ne, na ta ga ta sauke nauyin amanar da Allah ya ɗora mata.

Sharu Nata’ala Isma’il ya ce yanzu saboda tsari da suke da shi a masarautar kasuwar Ƙofar Wambai kafin a ga sun fita da wani al’amari waje na matsalar da ta shafi tsakanin ‘yan kasuwa zuwa wajen jami’an ‘yan sanda ko Alƙali yana da wuya saboda yadda masarautar ta baza wakilai saƙo-saƙo ake daidaita tsakani da yin sulhu idan wani abu ya taso.

Alhaji Sharu Nata’ala Isma’il ya shawarci sabon Magajin Garin kasuwar Ƙofar Wambai Ibrahim Ɗan Amana a kan nauyi da amanar da aka ɗora masa ya yi aiki bisa gaskiya da riƙon amana kamar yadda dama jama’a suka shaide shi a kai. Su kuma al’umma su ba shi haɗin kai domin cimma nasara.

Ita ma a nata ɓangaren mai ɗakin sabon Magajin Garin kasuwar Ƙofar Wambai, Hajiya Maryam Lawan Ɗanladi ta bayyana mutuƙar farin cikinta bisa zaɓo mai gidanta da aka yi a cikin dubbai aka ba shi wannan matsayi.

Ta ce suna yi wa Allah godiya bisa wannan tare da masoya.

Shi kuma ta yi addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyi da aka ɗora masa.

Hajiya Maryam Lawan Danladi ta jaddada yi wa mai gidan nata Alhaji Ibrahim Lawan Ɗan Amana addu’a da fatan sauke nauyi da Allah ya ba shi.

Shi ma ɗaya daga cikin ‘yan’uwan sabon Magajin Garin kasuwar Ƙofar Wambai, Alhaji Falalu ya ce wannan rana ce ta farin ciki ga ‘yan kolin jihar Kano gaba ɗaya ba kawai na kasuwar Ƙofar Wambai ba. “Muna da kyakkyawan zato a kan wanda aka yi wa wannan naɗin, domin mutum ne mai kyakkyawar mu’amala da haƙuri,” in ji shi.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun