GWAMNA LAWAL YA YABA WA HUKUMAR TSARO TA DSS KAN KAMA MAKAMAI A ZAMFARA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) bisa yadda suka kama wasu makamai da ake jigilarsu zuwa jihar.

A ranar Talatar da ta gabata ne Daraktan Hukumar a jihar ta Zamfara ya baje kolin makamai da alburusai da aka kama ga gwamnan a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, makaman da aka kama sun haɗa da bindigar RPG, manyan bindigogin ‘Machine gun’ guda biyu, bindigogi ƙirar AK47 guda tara, bindigogi ƙirar pistol guda biyu, mujallar alburusai guda goma sha tara, da sama da ɗaiɗaikun alburusai guda dubu.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga.

“Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame.

“Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin jami’an tsaro.

“Za mu ci gaba da tallafa wa sojojin ta kowace hanya da za mu iya don ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

“Zan yi farin ciki sanin cewa yawancin wafannan miyagun ‘yan asalin Zamfara ne. Ba baƙi ba ne, kuma wannan mutumin da aka kama ba shi kaɗai ba ne. Mun sami ire-iren waɗannan a cikin ’yan makonnin da suka gabata, amma wannan shi ne kaɗai muke gabatarwa ga jama’a. Irin wannan kamun na faruwa a kullum.

“’Yan bindiga na raguwa a Zamfara. Mun ga haka. Na buƙaci al’ummar Zamfara da su bai wa sojoji dukkan goyon bayan da suka dace.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun