Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnatin jihar Kano na kan gaba wajen abin da ya shafi kyautata jin daɗin ma’aikata a ƙasar nan, shi ya sa ma’aikata suka fito suke nuna gamsuwa da tagomashi da ayyukan alkhairi da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yake tanadar musu a wannan taro na bukin ranar ma’aikata.
Manajan daraktan Hukumar KAROTA na jihar Kano, Injiniya Faisal Muhammad ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a taron ranar ma’aikata ta duniya a Kano.
Ya ja hankalin ma’aikatan jihar Kano a kan yin riƙo da gaskiya da yin adalci a duk wani aiki da suke. “Su mai da hankali a kan haƙƙi da sauke nauyi da Allah ya ɗora musu,” in ji shi.
Faisal ya ce dukkan wani ma’aikaci akwai alƙawari tsakaninsa da Ubangiji da al’ummarsa, saboda haka a tsaya a kiyaye wannan alƙawari domin jihar Kano ta cigaba a yi nasara a kan abin da aka sa a gaba.
Ya ce akwai shiri da mai girma Gwamna yake da shi na ɓullo da tsari na sauƙaƙa harkar sufuri ga al’ummar jihar Kano kamar yadda aka samar ake sauƙaƙawa ɗalibai ta hanyar samar musu motoci.
Shugaban na Hukumar KAROTA, ya ce sauran al’umma ma akwai shirin da Gwamnan jihar Kano da Kwamishinan Sufuri suka yi masu a kan yadda za a samar da motoci da za su sauƙaƙa zirga-zirga cikin rahusa ba tare da al’umma sun jigata ba, ganin irin halin da al’umma ke ciki na matsin rayuwa.






