Daga Ibrahim Muhammad
Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta dakatar da nuna wasu manyan finafinan guda 22 masu dogon zango.
Shugaban Hukumar, Abba El-mustapha ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya raba wa manema labarai.
Ya ce gwamnatin jihar Kano ta ɗauki matakin ne a ƙoƙarinta na tabbatar da ana bin dokar tace finafina sau da ƙafa, tare da ƙara ɗora masana’antar Kannywood a kan turba madaidaiciya.
A cewar sanarwar, “An ɗauki wannan matakin ne biyo bayan tattaunawa da manyan jami’an Hukumar, tare da dogon nazari da aka yi. domin kawo ƙarshen ƙorafe-ƙorafen da ake yawan karɓa don ƙara inganta ayyukan Hukumar, tare da masana’antar Kannywood”.
Sunayen finafinan da aka dakatar sune:-
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Daɗin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro
Shugaban Hukumar ya ce, doka ce ta ba su damar tace duk wani fim, tare da lura da ayyukan masana’antar Kannywood matsawar suna da rijista da Hukumar a ko’ina suke. Don haka ya shawarci masu ɗaukar nauyin finafinan da su tabbatar da bin wannan doka da dakatar da saka finafinan a gidajen talabijin da kafar sadarwa.
Haka kuma ana sanar da su cewa su miƙo finafinan ga Hukumar domin tantance su, tare da ba su shaidar inganci ta tacewa nan da mako ɗaya mai zuwa, wato daga Litinin 19-25, Mayu, 2025, domin gujewa fushin doka.
Hukumar ta nemi haɗin kan dukkannin gidajen talabijin da Hukumar da ke lura da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa (NBC), kan su ci gaba da taimaka mata domin samun nasarar abin da ta sa a gaba na tsaftace jihar Kano da masana’antar Kannywood.






