Sarkin Kano Muhammad Sunusi II Ya Jinjina Wa Hukumar Hisbah

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban Gudanarwa na Hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheik Shehi Shehi Maihula, tare da babban kwamandar Hukumar, Dakta Aminu Ibrahim Daurawa, sun kai ziyarar girmamawa ga mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi II a fadarsa.

Ziyarar na daga cikin bikin cikar Hukumar Hisbah ta jihar Kano shekaru 25 da kafuwa

‎Da yake jawabi, Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce, sun kai wannan ziyarar ne tare da dukkan shugabannin Hukumar Gudanarwar na Hisbah.

Sheikh Aminu Daurawa, ya ce, yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa domin samar da makaranta da za ta riƙa horar da jami’an Hisbah, domin ƙara ƙarfafa hazaƙarsu kan sha’anin harkokin ayyukansu na samar da tsaro.

‎‎A jawabin mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya bayyana gamsuwarsa ga aikace-aikace Hukumar ta Hisbah, musamman a ƙoƙarinta na daƙile ayyukan baɗala a tsakanin al’umma.

Malam Muhammad Sunusi II ya buƙaci Hisbah ta samar da tsari da zai taimaka wajen ƙara wanzuwar haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi, musamman ma malaman addinin Musulunci.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal