Tsofaffin Ɗaliban Rukunin Makarantun Alhaji Abdullahi Ɗanbatta Sun Yi Taron Sada Zumunta

Daga Ibrahim Muhammad

Tsofaiffin ɗaliban rukunin makarantun marigayi Alhaji Abdullahi Ɗanbatta, Fuƙara’u Ƙofar Ruwa Sakandire da na Kwalejin Assahabah sun gudanar da taro da karrama waɗanda suka ba da gudunmuwa ga cigaban makarantun.

Taron shi ne karonsa na farko tun kafa makarantun, ya sami halartar tsoffin ɗalibanta da dama, Alhaji Maulud Abdullahi Ɗanbatta, wanda ɗa ne ga wanda ya assasa makarantun, kuma shi ne shugaban Ƙwalejin Assahaba ya bayyana farin cikinsu da taron.

Maulud ya ce mahaifinsu ya kafa makarantar ne a matsayin ta Allo da ta fara da Malami ɗaya, Malam Ma’azu yana koyar da ‘ya’yan gidansu da na maƙwabto.

Makarantar ta fara da ta Ƙur’ani ta zama ta Firamare har gwamnati ta turo hedimasta na farko, Malam Nasidi Fagge, ɗalibai da aka yaye rukunin makarantun akwai manyan ma’aikata da jami’an tsaro da manyan malamai da sauran fannoni.

Alhaji Maulud Abdullahi Ɗanbatta ya ce tsawon lokaci sama da shekaru 40 wani bai ga wani ba a ɗaliban makarantar, sai yanzu da suka haɗu a fuskoki da yin fatan alheai da kuma yi wa mahaifinsu da ya assasa makarantar marigayi Alhaji Abdullahi Ɗanbatta addu’a da duba halin da makaranta take ciki da yadda za a taimaka mata.

Ya yi kira ga tsaffin ɗaliban su waiwayi makarantar domin tallafa mata duba da yadda suka mori makarantar su yi koyi da jajircewar wanda ya gina makarantar, ya kuma ba da rayuwarsa gaba ɗaya ga cigaban ta da ‘ya’yan talakawa shi ya sa ma ya sa sunan makarantar na asali Fuƙara’ul Musulmin.

A yayin taron wasu ɗalibai sun bayar da gudunmuwa domin cigaban makarantar ciki har da Alhaji Maulud da ya bayar da fili don gina makarantar dare da mahaifinsu ya so samarwa tun yana raye. Shi ma Alhaji Abdullahi Ƙofa ya yi alƙawarin gina ajujuwa guda biyu. Haka Hajiya Hafsat Hamidu Ali Madigawa ta yi alƙawarin samar da kujerun zama a makarantar tare da bayar da gudunmuwar kuɗi a madadin ‘yan ajinsu.

A yayin taron an ba da lambar yabo ga marigayi Alhaji Abdullahi Ɗanbatta da ya assasa makarantun da shugaban makarantar na farko, Malam Nasidi Khalil Fagge da ƙungiyar Injiniyoyi Mata da sauran mutane da suka ba da gudunmuwa ga cigaban makarantar.

  • Related Posts

    WOTCOSA Ajin 1975 A Shekara 50: Sun Karrama Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje Da Tagwayen Lambobin Yabo

    Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban tsohuwar makarantar horon malamai ta mata ta Kano (WTC), Women Teachers College Old Girls Association (WOTCOSA) da yanzu ake kiran a makarantar da Goverment Girls College (WTC)…

    Ɗaliban Ƙaramar Hukumar Dala Da Gwamnatin Kano Za Ta Tura Manyan Jami’o’i Na Cikin Gida Da Ƙasashen Waje Karatun Digiri Na Biyu, Sun Yi Taron Nuna Godiya

    Daga Ibrahim Muhammad Ɗalibai ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala da za su tafi karatu manyan jami’o’i a ciki da wajen ƙasar nan da gwamnatiin jihar Kano ta ɗauki nauyinsu sun…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal