Daga Ibrahim Muhammad
Muhammad Bello Shehu Fagge lauya ne mai kwazo kuma mutum ne mai kishi da son ganin cigaban al’umma musamman matasa wajen dogaro dakai da kuma neman Ilimi ya dade yana bada gudunmawa don ganin ya kyautata tsari na bunkasa ilimi da cigaban matasa ga al’ummar mazavarsa ta karamar hukumar Fagge.
Daga irin gudunmawa da yake baiwa cigaban ilimi sun hada da mayar da yara makarantu da daukar dawainiyarsu da kuma tallafawa dinbin yan makarantu da zasu dauki jarabawar karshe na gama makarantun gaba da firamare maza da mata da kuma da biyawa masu zuwa manyan makarantu kudin rijista da sauran hidima da ake.
Wannan tasa al’ummar ƙaramar hukumar fagge suka yaba da jin dadin irin wannan kyakkyawan gudummawa da yake bayarwa na kokarin gina masu tasowa akan ilimi wanda shine kashin bayan kowane irin cigaba har ma suke masa lakabi da garkuwar ilimi.Duk irin wannan kokarin kishi ne da yake dashi na kansa ba tare da yana rike da wani matsayi ba, duk abinda yake daga aljihunsa ne.
Irin wannan gudunmuwa da Barista Muhammad Bello Shehu yake bayarwa ta dada masa kima da yarda da aminci daga al’ummar. Karamar Hukumar Fagge don haka da yake yana siyasa suka ga cancantar su sashi a gaba domin suna da kyakkyawan fata akan sa na ganin yanda yake hidimta musu a kashin kansa, idan ya sami wata dama zai yi musu fin abinda yake musu a fannoni da dama a harkar bunkasa cigaban rayuwa.
Wannan tasa suka ga dacewa da cancantar su mara masa baya a siyasa da yake ta bashi hadin kai da goyon baya da har ta kai yayi nasarar zama ɗan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Fagge a zaben 2023 wanda yanzu shekara biyu kenan yake wakilci a majalisar tarayya.
Akwai magana da ake fada cewa mai kamar zuwa kan aika zuwan Hon.Barista M.B.Shehu majalisar tarayya cikin shekaru biyu yana taka rawar gani sosai da al’umma bama a kano ba sun shaida yana daga yan majalisa da ya fito daga arewa da yake kai kuɗirori wanda suke da alaƙa ta kai tsaye da talakan Najeriya da ya shafi cigaban ƴan kasuwa, ɗalibai da matasa.
Daga irin kudurce kudurce da yake kaiwa ko a yan kwanakin nan yakai kudiri akan halin da ƴan Najeriya mazauna Saudiyya ke ciki.sannan ya kai kudiri domin daƙile yunkurin babban bankin Najeriya (CBN) na cazar 0.5%akan dukkan nin hada-hadar kuɗi yayi rawar gani kai kudiri akan tsarin gudanarwa ta yanar gizo-gizo da hukumar shige-da fice ta ƙasa ke yi, (E-pasport) Wannan kaɗan kenan daga cikin iri gudummawar da yake badawava fanni tallalin arziƙin ƙasa.
Haka ma a fannin ilimi dan majalisar ya kai kudiri na neman samar da jami’ar kula da lafiyar haƙori a Fagge.
MB she yadinkawa ƴan firamare kaya makaranta kala 3500 yana biyawa ɗalibai fiye da ₦56,000,000.00 kuɗin makaranta duk shekara. Da gina makaratu daban-daban kamar su Mai ɗorewa
na tsugunne Islamiyya a barikin sojojin sama.
Hon.Muhammad Bello shehu yana taka rawa a fannin bunkasa lafiya har ya kai kudiri domin samar da cibiyar lura da kiwon lafiya, (Federal Medical Center, Fagge) da a yanzu haka ya tsallake karatu na uku.Sannan yasa an rushe asibitin Sabo Garba dake Fagge ana kan aikin zamanantar dashi a dada fadada shi a samar da kayan aikin kula da Lafiya na zamani.
Cikin irin ayyuka .da majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Fagge ke aiwatarwa sun hada da kokarin kyautata fannin tsaro ya sanya fitilu masu aikin da hasken rana kimanin 1,857 a sako da lunguna na ƙaramar hukumar .Ga kuma kokarin gina dan’adam ya ya samawa matasa fiye da 50 aikin a hukumomin tsaro daban-daban ya samarwan wasu matasan 76 ayukka a jami’o’i da sauran wurare .
Hon Muhammad Bello Shehu Fagge a kokarinsa don bunkasa kasuwanci da ƙananan sana’oi a tsakanin al’umma, ya yi gagarumin tallafi da a baya ba a sami wani dan majalisa da bai wuce shekara biyu ba ya yi kamar nasa domin shine ya tallafawa matasa 3000 a da abubuwa daban-daban da suka hada da kekunan Ɗinkin na zamani da injunan yin walda dana bayar da wuta hatta kanikawa an samar musu da akwatunan kayan na zamani. Daga irin tallafi da dan majalisar tarayya na karamar hukumar Fagge ya bayar sun hada da Babura,Motoci,Firji da kuma jari ga mutane 2000.Sanna ya cigaba da batar da wannan tallafin duk mako.
Sannan ya na taba katifu musamman ga amaren da za suyi aure kusan duk mako a fannin addini yana gina masallatai yanzu haka yana gina sabon masallacin Juma’a na Kashahara da kuma sawa masallatai daban-daban fitila masu aiki da hasken rana don yin ibada cikin nutsuwa. Yana kuma kokarin samar da ingantaccen ruwan sha ta gina rijiyoyin burtsatse a wurare daban-daban da gudanar da tsaftace muhalli ta sawa a yashe kwatar kwarin Gogau da gina babbar magudanar ruwa data ratsa mazabar kwaciri
A fannin kyautatawa, MB Shehu yana raba fiye ɗa zunzurutun kudi ₦7,000,000.00 a duk mako a makarantu domin yin saukar Alkur’anin.Ya gina runfuna na zamani masu dinbin ga masu sana’oi daban-daban.
Sannan an soma gudanar da aikin tituna guda 12 a Fagge wadannan kadan ne daga cikin irin dinbin ayyuka da dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Fagge.Hon.Barista Muhammad Bello Shehu yake gudanarwa a cikin shekaru biyu da zuwan sa majalisa in akayi la’akari da yanda ake tura wakilci a baya shekara biyun dan majalisar ya amfanar da alummar fagge fiye da wadanda suka shafe shekaru suna wakiltar Fagge a baya.
Nazir Saminu Ibrahim wanda daya ne daga hadimai ga dan majalisar tarayya na Fagge a bangaren yada labarai ya tabbatar man da cewa Wannan nasara ce gagaruma ga al’ummar Ƙaramar hukumar fagge da suka tura mutum mai kishin don cigabansu suke kuma soma girbar sakamakon wakilcinda yake musu ta kawo da gudanar da muhimman ayyuka cikin shekaru biyu suna da yakinin nan da sauran shekaru kafin a shiga zabe karamar hukumar Fagge zata zama abin kwatance a fannin cigaban da dan majalisar su na tarayya Muhammad Bello Shehu zai cigaba da kawo musu.








