Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana rashin fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata da cewa ba rashi ne ga al’ummar jihar Kano ko Arewa ko Nijeriya kaɗai ba, rashi ne da aka yi wa duniya.
Shugaban kamfanin Hamir Global Venture, Alhaji Hamisu Rabi’u Jingau ne ya bayyana hakan a lokacin da yakai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a Unguwar Ƙoƙi.
Ya ce saboda Alhaji Aminu Ɗantata uba ne, kuma jagora ne ga dukkan al’umma, musamman su ‘yan kasuwa, haƙiƙa sun yi babban rashi na wannan bawan Allah, sai dai kurum babu wani abu da za su faɗa sai dai su yi masa addu’a da jaje ga ‘yan’uwa da iyalai da abokan arziƙi. Ya yi fatan Allah ya jiƙansa, ya gafarta masa.
Alhaji Hamisu Rabi’u Jingau ya ce, su ‘yan kasuwa ba su da wani jagora da suka sa a gaba lokacin da yake raye sama da Alhaji Aminu Ɗantata, dukkan matsalolinsu da suka taso waɗanda suka fi ƙarfinsu sukan zo gabansa su gaya masa, kuma ba su taɓa zuwa a iya sanin sa da wata matsala ba wacce bai saurare su ya yi musu maganinta ba, “Abubuwa sun faru ya shige mana gaba. Muna fata Allah ya yi masa rahama,” in ji Alhaji Hamisu Jingau.






