Daga Ibrahim Muhammad.
An jawo hankalin ‘yan kasuwar jihar Kano su tabbatar sun yi rijistar katin zaɓe da ake gudanarwa a halin yanzu duba da cewa mafi yawan al’ummar Kano ‘yan kasuwa ne.
Shugaban Dattawan ‘yan kasuwar Singa da Sabon Gari, Allhai Ibrahim Ɗanyaro ne ya yi kiran a yayin wani taro da aka gudanar da ya ƙunshi shugabannin kasuwannin jihar Kano gaba ɗaya don wayar musu da kai a kan muhimmancin mallakar katin zaɓe.
Ya ce yawancinsu duk wanda ya wuce shekara 18 suna da katin, amma akwai wasu samari da ba su yi katin ba har yanzu da suka kai shekarun yi, saboda haka ya kamata ‘yan kasuwa su wayar da kan ‘ya’yansu da ƙanne da abokan mu’amalarsu kowa ya tashi wanda ba shi da rijistar ya yi.
Ya ƙara da cewa idan akwai canji ko wani abin da kake so ka gyara na katin ko suna ko sauyin wurin zama duk yanzu an ba ka dama a matsayinka na ɗan ƙasa ka gyara rijistarka. A baya an sha yin irin wannan, amma ba a ga ‘yan kasuwa sun tashi tsaye wajen su wayarwa da ‘yan’uwansu kai ba a kan ya kamata a ce kowa ya fuskanci kansa.
Ya ce wannan kuma yana da dangantaka da halin da suke ɗaukar kansu ne, ya kamata ‘yan kasuwa su waye su san suna da wata rawa da za su iya takawa game da tafi da ƙasar nan gaba ɗaya. Don haka taron na wayar wa ‘yan kasuwa kai ne yadda ya kamata su san ‘yancinsu da muhimmancinsu da kuma ni’imar da Allah ya yi musu na yawa suna da rawa da za su taka. Sannan a harkar tattalin arziƙi akwai abin da ‘yan kasuwa ya kamata su kai shugabanci da za a yi a kowane yanayi a ƙasar nan ya zama suna da abin cewa ko yana da abin da yake so a ra’ayinsa wanda ya kamata a yi.
Ya ce akwai abokan tafiyar ‘yan kasuwa a ƙasar nan sune ma’aikata, kuma har jam’iyya ake da ita ta ma’aikata ya kamata su ma ‘yan kasuwa, ya zama sun girma da wayewar a ce suna da jam’iyyar ‘yan kasuwa kuma in aka duba shugaban Amurka mai ci ɗan kasuwa ne, ta yiwu da taimako yake bayarwa wasu su hau mulki, amma da ya juyi ya ga ya kamata shi ma ya taka rawar da kansa saboda muhimmancinsa da muhimmancin yi wa Amurka aiki ya yi shugaban ƙasa ya faɗi ya sake dawowa yanzu.
Alhaji Ibrahim Ɗanyaro ya ce wannan tunani ne da ya kamata ‘yan kasuwa su yi su sa wayewa da za su iya shiga ko’ina a dama da su na al’amuran ƙasa yadda su ma za su kawo tasu irin gudunmawar da za a gina cigaban ƙasa.
Shi ma a jawabinsa Alhaji Sabi’u Baƙo ya ja hankalin ‘yan kasuwa kan muhimmancin yin rijistar duba da jihar Kano na da tarin ‘yan kasuwa fiye da kowace jiha a Nijeriya, suna da kuma irin gudunmawar da za su bayar a siyasa. “Don haka kowane ɗan kasuwa ya yi ƙoƙari ya sa ‘ya’yansa da ma’aikatansa da duk waɗanda suke ƙarƙashinsa sun yi rijista domin ba su da bakin magana idan ba su da rijistar nan,” in ji Alhaji Baƙo.
Ya ce idan aka yi rijistar nan za ta yi wa jihar Kano rana idan Allah ya taimake mu idan aka sami rijista sama da miliyan ɗaya ko biyu ko wani abu kamar haka ko gwamnatin tarayya ma suna da abin da za su ce kar su ɗauka kawai Kano ita ce mazaɓarsu su ɗauka duk Nijeriya suke so su taka rawa, kuma Kano ita ce mabudi na farko, don babu wata jihar da ta yi irin wannan taro na faɗakar da ‘yan kasuwa a kan muhimmancin yin rijista.
Shi ma shugaban shugabannin ƙungiyoyin kasuwanin Kano Shugaban ƙungiyar kasuwar Singa Batista Zakari Junaid ya ce, taron an sami nasarar gudanar da shi cikin nasara, domin ‘yan kasuwa sun halarta, an yi ƙoƙarin wayar da kansu domin samar da rijista da kuma irin muhimmancinta ga taimakawa ‘yan kasuwa wajen haɓaka arzikiinsu da jin sautin muryoyinsu lokacin da suke ba da buƙata a wajen gwamnati.
Taron ya samu halartar manyan ‘yan kasuwa da dama daga kasuwanni daban-daban ba jihar Kano, kuma an gabatar da jawabai a kan muhimmancin yin katin zaɓen ga ‘yan kasuwa.
Cikin waɗanda suka yi jawabi akwai Alhaji Rabi’u Hamisu Jingau, wani fitaccen ɗan kasuwa a kasuwar Singa da kuma Alhaji Sa’id Dattijo Adahama da sauran ‘yan kasuwa da dama.








