Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban ƙaramar hukumar Ɓagwai Hon. Bello Abdullahi Gadanya ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam bisa shirya taron kalankuwa na nuna al’adu na gargajiya da sana’oi da ake tun kaka da kakanni.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a rumfar ƙaramar hukumar Ɓagwai da suka baje kolin kayayyaki da suke nomawa.
Ya ce sun kawo abin da suke nomawa a yankin da ke da tasiri a noma da kawo abin da suke da su na gargajiya sun baje kolinsu jama’a sun gani.
Shugaban na ƙaramar hukumar na Ɓagwai ya nuni da cewa yankin ya yi fice wajen noma rani da damina, suna da katafaren dam da suke noma kayan lambu da kiwon kifi, ko a ‘yan kwanaki baya ma ya jagoranci zuba jarin kifi a dam ɗin don a samar da kifi mai yawa.
Hon. Bello Abdullahi Gadanya ya ce irin wannan taro na nuna al’adu, mataki ne na inganta kimar al’ummarmu da nuna irin sana’o’i da muka gada muke alfahari da wanzuwarsu har yanzu kuma zai amfanar da matasa masu tasowa.

