Daga Ibrahim Muhammad
Ƙungiyar ‘yan kasuwar Galadima ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman, sun gudanar da aikin gyaran titin kasuwar da ya taso daga kwanar kasuwar zuwa kan titin Faransa.
Shugaban kasuwar Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya ce dama kwaltar titin da ya cike da tarin ƙasa ya daɗe yana damunsu, kuma kasancewar titin babba ne da gwamnati ta kashe maƙudan kuɗi ta yi shi ne domin amfaninsu, datti da ƙasa da ke tasowa ta zo ta lulluɓe shi ba a ma ganin kwaltar, kuma sune ke amfana da titin don haka ba za su ce sai sun jira gwamnati ta zo ta gyara masu ba.
Ya ce shi ne sai suka yi hoɓɓasa a matsayinsu na shugabancin kasuwa da taimakon Sarkin kasuwa, suka haɗu da jama’ar kasuwa, kowa ya ba da gudunmuwa irin wanda zai iya aka nemo kamfani aka yi lada da shi zai haƙe da tattare ƙasa da ta dandaɓe a titin ya kwashe shi kamar yadda ake aikin a halin yanzu.
Ya ce aiki ne da kowane ɗan kasuwa ya ba da gudunmuwa ake yi suna zuwa suna ganin yaɗda aiki ke tafiya, kuma yanzu wannan gyara da suka yi, za su sa mutane su kiyaye kar ya bar ƙasa ta dawo kan titi. “Za mu sa kowa ya daɓe ƙofar shagonsa da siminti yadda ƙasa ba za ta riƙa taruwa ba har ta gangara ta cike titin.
Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya ce sun gayyato ‘yan sanda da hukumomin kiyaye haɗɗura (Road Safety) da KAROTA da malaman tsafta na matakin ƙaramar hukumar Fagge, da na jihar Kano sun kuma sanar da majalisar ƙaramar hukumar Fagge da manajan daraktan kasuwar Abubakar Rimi, Galadima da Singa don haka hukuma ma ta san da aikin, kuma ta yaba musu a kai.






