Daga Ibrahim Muhammad
Ƙungiyar Lauyoyi ‘yan asalin jihar Kano ta ƙasa ta aika wa shugabannin Majalisar Dattawa da na Wakilai ta ƙasa takardun ƙorafi da neman cigaba da bincike kan Hon. Alasan Ado Doguwa bisa zargin hannu a kisan da aka yi wa mutane a ƙaramar hukumar Tudun Wada yayin zaɓen 2023.

Lauyoyin sun bayyana cewa lamarin ya janyo mutuwar mutane da dama, don haka suke kira ga Majalisun na Ƙasa su saka baki domin tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Ƙungiyar ta roƙi kwamitocin shari’a, ‘yan sanda, da na kare haƙƙoƙin ɗan’adam su shiga cikin binciken, domin samar da adalci ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka ji raunuka.
Haka kuma, sun buƙaci shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai da su shirya taron jin ra’ayin jama’a, ko kuma su nemi cikakken rahoto daga rundunar ‘yan sanda ko ma’aikatar Shari’a ta jihar Kano.
Ƙungiyar ta ja hankali da cewa a tsarin mulkin dimokuraɗiyya babu wani da ya fi ƙarfin sharia, rashin yin adalci ko barin wannan zargi ya tafi ba tare da bincike mai zurfi ba, hakan take doka ne, kuma zai lalata tsarin shari’a.
Lauyoyi sun gabatar da takardar ne biyo bayan kai takarda ofishin Kwamishinan Sharia na Kano da hotunan waɗanda lamarin ya shafa, don haka ne suka kawowa tagwayen majalisun wanan ƙorafi don ɗaukar mataki
A ƙarshe, Lauya Dakta Jafar Sadik, wanda ya sanya hannu a madadin ƙungiyar ya ce yana fatan Majalisun za su bibiyi haƙƙin jama’ar.






