Sat. May 10th, 2025

Ɗalibai 173 Na Makarantar Babban Malami Madabo Islamiyya Sun Yi Saukar Alƙur’ani

By Saleh Aliyu Apr 28, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Makarantar Babban Malami Madabo Islamiyya ta gudanar da taron yaye ɗalibai da suka yi saukar karatun a ranar Lahadi a ɗakin taro na gidan Mumbayya.

Shugaban makarantar kuma Darakta na makarantun Khulafa’ur Rashiduna da ke jihar Kano guda 12.

Malam Nassar Rilwan Ibrahim Babban Malami ya ce ɗalibai 173 ne maza da mata suka sauke Alƙur’ani da Riwayar Hatsu da kuma guda 16 da suka yi riwayar Warshu aka yaye.

Ya ce saukar karatu a makarantar wannan shi ne karo na 24 tun daga kafa ta, domin da an soma yin ta da dare ne a 1960 a lokacin.

Babban Malami na Madabo, Malam Ibrahim daga baya kuma a 1983 Shaikh Rilwan Ibrahim Babban Malami ya buɗe na karatun yamma kamar irin wannnan ke nan ake tara samari maza da mata don koyar da su Alƙur’ani da sauran darussa na Islamiyya wanda yanzu suna da malamai guda 40.

Malam Nassar Rilwan Ibrahim ya ce, yanzu haka makarantar tana da mazauni domin sun sami gudunmawa daga Hajiya Mariya Sanusi Ɗantata, ta ba da ginin makaranta mai ajujuwa takwas da makewayi guda huɗu da ofisoshi biyu.

Shi ma Bashir Mudi ya ba da ginenniyar makaranta.

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala, marigayi Ali ‘Yantandu, shi ma ya sayawa makaranta wuri ya gina.

Ya ƙara da cewa daga waɗanda suka tallafa wa makarantar akwai Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya gina mata rukunin ajujuwa biyu.

Tsohon Gwamnan Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje shi ma ya ba da tallafi na Naira miliyan 10, an sai wa makarantar wurare.

Haka Alhaji Aminu Ɗantata ya ba da gudunmawar Naira miliyan₦10 an fara gina wuraren da su, amma ba a kai ga kammalawa ba.

Ya ce yanzu matsalolin da suke fuskanta sune na ginin da suka fara ba a kammala ba suke so su ga an ƙarasa su da kuma gyara ginin da Kabiru Gaya da wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala suka yi musu don sun yi rauni suke son a yi musu kwaskwarima a inganta su.

Malam Nassar Rilwan Ibrahim ya ce, sun kai takarda ta neman tallafin a zo a ƙarasa musu wannan ginin makarantar ga zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na wanda yake bai wa cigaban ilimi kulawa ta musamman suna nan suna bibiya suna fatan Gwamna da gwamnatinsa za su duba koke na wannan makaranta ta ga cewa ta share musu hawaye.

Ya ce tunda aka buɗe makarantar tasu a shekarar 1983 zuwa yanzu an sami nasarori har ana sauka ana yaye ɗalibai har karo 24 da a cikinsu akwai mahaddata, akwai waɗanda sun zama Gwanaye na Alƙur’ani. Wannnan nasara ya samu ne bisa irin haɗin kai da iyayen yara ke bai wa makaranta suna godiya da irin haɗin kai da ake ba su.

Malam Nassar Rilwan Ibrahim Babban malami ya yi kira ga al’umma, musamman waɗanda Allah ya horewa su riƙa taimakawa irin waɗannan makarantu na Islamiyya su ga cewa sun kawo gudunmawa ta yadda karatun ‘ya’yansu da tarbiyyarsu za ta gudana yadda ya kamata.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *