Daga Ibrahim Muhammad
A ƙoƙarinsa na tallafa wa harkar tsaro a mazaɓun ƙananan hukumomin Haɗejia, Auyo da Kafin Hausa da Hon. Usman Ibrahim Kamfani yake wakilta a Majalisar Tarayya ya tallafa wa jami’an tsaro da babura domin inganta ayyukansu.
Taron da aka yi na raba baburan guda 32 da ɗan majalisar ya samar da Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Namadi Ɗanmodi ya sami halartar gudanar da shi a ƙaramar hukumar Auyo a makon da ya gabata.
A jawabinsa, Gwamnan na Jigawa, Alhaji Namadi Ɗanmodi ya yaba da ƙwazon ɗan majalisar Usman Kamfani bisa irin ƙoƙari da yake wajen kawo ayyuka daban-daban na kyautata cigaban al’ummarsa. Wannan tallafi kuma da ya bayar ga hukumomin tsaro na babura zai taimaka musu wajen inganta harkokin tsaro.
Gwamnan ya yi kira ga sauran mutane musamman masu riƙe da muƙamai da masu iko su yi koyi da ɗan majalisar wajen ba da gudunmuwa da za su iya domin taimaka wa jami’an tsaro ta yadda za su sami yanayi mai kyau na gudanar da ayyukansu na ba da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
A jawabinsa ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Hadejia, Kafin Hausa da Auyo Hon. Usman Ibrahim Kamfani ya ce an samar da babura ne guda 32 domin taimakawa ayyukan da hukumomin tsaron suke domin kai ɗauki cikin gaggawa duba da halin da ake ciki na tsadar mai sannan kuma ba kowane saƙo da lungu ne mota za ta iya shiga ba.
Hon. Auyo ya ƙara da cewa waɗannan mashina suna fata za su tallafa wajen sauƙaƙawa jami’an tsaron gudanar da aikinsu cikin gaggawa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.
An dai raba baburan ne ga hukumomin jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da jami’an kula da tsaron al’umma “Civil Defence” da na yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da na shige da fice.
Da yake ƙarin haske game da ayyukan ɗan majalisar babban hadiminsa Idris Ɗan Makama Namatasa Auyo ya ce, kishin ɗan majalisar nasu na tarayya, Hon. Usman Ibrahim na ganin an kyautata tsaro ne ta sa ya ɗauki wannan mataki na sake tallafa wa hukumomin tsaron a wannnan karon domin dama yana ba da gudunmuwa ta inganta tsaro a matakai da dama.
Ya ce haka yake tallafawa da yin ayyuka a fannoni na bunƙasa rayuwar al’umma da inganta harkar noma da lafiya da cigaban ilmi yayin da hakan ya amfanar da al’ummarsa hakan tasa al’umma suka aminta da wakilcin da yake musu, suke daɗa zaɓensa duk lokacin da zaɓe ya zo. “Dan haka ma yanzu ma babu ‘yan hamayya a mazaɓarsa” in ji shi.
Idris Ɗan Makama Namatasa Auyo, ya yi kira ga al’umomin Haɗejia, Auyo da Kafin Hausa su cigaba da bai wa ɗan majalisar nasu na tarayya Usman Ibrahim Kamfani da gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Alhaji Namadi Ɗanmodi haɗin kai da goyon baya domin cigaba da amfana daga irin ɗimbin ayyukan na cigaba da ake gudanarwa.






