Daga Ibrahim Muhammad
A ƙoƙarinsa na kishin bunƙasa ilimin addinin Musulunci, Ɗan Masanin Ƙauran Namoda, Alhaji Sahabi Usman zai gina katafariyar babbar makaranta ta nazarin ilimin addini da aka sa wa suna Sahabi Liman Academy a garin na Ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara.
Za a gudanar da taron aza tubalin gina cibiyar ne a harabar filin da ke a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda.
Wannan tasa mutane da dama suke nuna mutuƙar farin ciki da jin daɗinsu ga wannan babban abin alkhairi daya kawo wa yankin.
Da ma akwai ma ginin katafaren masallacin Juma’a da Alhaji Sahabi Liman yake ginawa da zai ɗauki yawan masallata 12,000 idan aka kammala shi.
Mutane da dama da muka zanta da su sun bayyana cewa wannan aikin na alkhari dama Ɗan Masanin na Ƙauran Namoda, Alhaji Sahabi Liman ya saba aiwatarwa domin mutum ne da kullum yake kyautatawa cigaban al’umma.