Daga Ibrahim Muhammad
Duba da yadda al’amuran rayuwa suka sauya a ƙasar nan da mutane suka tsinci kansu a yanayi da ba a taɓa tsammani ba, an yi kira ga al’umma su jajirce su yi juriya da yin addu’a Allah zai kawo mafita daga halin da ake ciki.
Manajan kamfanin sarrafa ruwan leda na LUCKY da ke rukunin masana’antu na Dawakin Dakata, Alhaji Muhammad Yusuf ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a Kano, inda ya yi nuni da cewa shi shugabanci amana ce wanda yake ya tabbatar akwai lokacin da Ubangiji zai tambaye shi amanar da ya damƙa masa. “Ya kamata shugabanni su yi hattara su kiyaye su dubi amana da Allah ya ba su, ba don sun fi wani ba, su ya zaɓa don ya jarraba su, su tsaya su dubi Allah su yi jagoranci bisa amana da adalci,” ya jaddada.
Ya ce halin da talakawa suke ciki yanzu an kai wani yanayi mai tsauri abin babu daɗi shugabanni su dubi Allah su yi nazari a kan hanyoyi da za su bi su fitar da mutane daga mawuyacin hali da suke ciki.
Da ya juya kan masana’antu ya ce yanzu abubuwa sun zama babu daɗi, ana fama da matsalar wuta da tsadar kayayyakin sarrafawa, amma babban ƙalubale a gare su da suka fi fuskanta shi ne matsalar wuta domin daga watan Agusta na bara sai da aka nunka kuɗin wuta sau uku daga yadda ake biya ₦71,50 sai da ya koma ₦209, idan aka haɗa har VAT ma duk ‘unit’ ɗaya ya kai ₦226. Wannnan ne halin da aka tsinci kai,” in ji shi.
Ya ce, “Idan kana biyan ₦250,000 sai ka biya sama da ₦700,000 wanda ta kai a rukunin masana’antun suna Dawaki Dakata akwai mutanen da yawa sun rufe sana’ar sun haƙura. An yi ƙa’ida da kamfanin rarraba wutar za a riƙa ba da wutar a ‘Ban A’ saboda sun raba abin kashi-kashi ne. Akwai ban A da B da C. Idan kana ban A za ka sami wuta na awa 20 a wuni, amma takan kai wata rana ma ba za ka sami wutar awa takwas ba. Har ta kai a mako suna a ‘Ban A’ amma ba sa samun wuta ta kwana uku, amma za a kawo musu bill a kuɗin ‘ban A.’
Ya yi nuni da cewa ba yadda za su yi domin sun yi ƙorafe-ƙorafe ga waɗanda abin yake hannunsu, amma ba wani sauyi. Wannan na daga manyan ƙalubale da masana’antu ke fuskanta. Haka a ɓangaren kayan aiki shi kansa yana tsada, musamman su masu yin ruwa leda da ake saye a baya Naira miliyan ɗaya, yanzu sai ka sa sama da da miliyan uku, haka ake tafiya harkokin babu daɗi ana yi ya fi a ce ba a yi.
Alhaji Muhammad Yusuf Manajan kamfanin sarrafawa ruwan leda na LUCKY ya ce, wannan ta sa abubuwa suke raguwa, “Hatta a ma’aikata, ba za ka iya ɗaukar masu yawa ba, duk abubuwa da kake iya yi a baya yanzu ba zai yiwu ba, ko yanayi na buƙatun da za a ce yau an yi kaza, an yi kaza, ko motarka ta tsufa da take kai maka kaya ka sayar da ita ka ƙara kuɗi ka sayi sabuwa ya gagara. Yanzu gidan ruwa ba kowanne ba ne ya isa ya cire kuɗi a lokaci ɗaya ya je ya sayo motar ɗaukar kaya ba, sai dai wacce kake da ita ka lallaɓata,” ya bayyana.






