Daga Ibrahim Muhammad Kano
Mai ɗakin Gwamnan Jigawa.,Hajiya Amina Umar Namadi Ɗan Modi ta bayyana rasuwar Galadiman Kano Abbas Sanusi da cewa babban rashi ne saboda Uba ne baga ‘ya’yansa ko jama’ar Kano kawai ba ga dukkan al’ummar ƙasa.
Ta bayyana haka ne da take zantawa da ‘yan jarida a da ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Galadiman Kano Abbas Sanusi a gidansa.
Ta ce Galadima mutum ne mai haƙuri idan da kowa zai koyi da haƙuri to kowane mutum zai dace a rayuwarsa.
Hajiya Amina Umar Namadi Ɗanmodi ta ce a matsayinta ta matar Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi da kuma jama’ar jihar gaba ɗíaya suna mika ta’aziiyya ga jama’ar jihar Kano da na ƙasa baki daya da ahalin marigayi Galadiman Kano.






