Sat. May 10th, 2025

An Karrama Shugaban NNPP Na Kano Dakta Hashim Sulaiman

By Saleh Aliyu Apr 8, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Arewa Media Foundation And Development, ta karrama shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa saboda kyakkyawan jagoranci da kawo cigaban al’umma da kuma son zaman lafiya.

A jawabinsa bayan karɓar shaidar yabon, wanda sakataren Arewa Media Foundation And Development, Sulaiman Ahmad ya miƙa masa a madadin Shehu Usman shugabansu, Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa ya nuna mutuƙar godiya ga Allah da gidauniyar ‘yan jaridar bisa karramawa da ta yi masa, wanda ba shi kaɗai ko NNPP aka yi wa ba, al’ummar Kano aka bai wa domin don su suke irin abubuwan da suke ake gani na cigaba ba domin kawunansu ba.

Ya ce ya tabbatar jagoransu Sanata Dakta Rabu Musa Kwankwaso da zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf su ma wannan lambar yabo kamar su aka bai wa, domin da yawa al’ummar jihar Kano da suke mata fatan alheri da son zaman lafiya haɓɓakar tattalin arziƙinta za su yi alfahari da wannan lambar yabo da aka bai wa jam’iyar NNPP da ta fi kowace son zaman lafiya a faɗin ƙasar nan da ma jihar Kano.

Ya ce suna gode wa Allah domin dukkan abubuwa da suka faru na rashin jin daɗi a jihar Kano kowa ya san ba da hannunsu ba ne, musamnan harkar masarauta sun zo sun tarar ana sa sarakuna na cikin birni da na ƙauyuka, su kuma suka ce a bi tarihi yadda yake, inda yake da Sarki a mayar musu, tunda an riga an yi wancan abubuwa.

Ya ƙara da cewa suka dawo da Sarkin Gaya kowa ya san da shi dama a tarihi da na Rano da na Ƙaraye duk da su a tarihi, amma Bichi da ba ta ta ba yin Sarki ba, suka ce ta koma yadda take na Hakimi da ma cikin birni Sarkin Kano shi ne ƙwaya ɗaya.

Ya ce amma abubuwa irin wannan suka haɗu da mutane marasa daraja wanda Kano ta ci da su ta sha da su ta ba su ilimi, sun ƙoshi da abinci, amma ba su ƙoshi da hankali ba, kullum rashin albarka da rashin mutunci shi suke gabatarwa a jihar Kano.

Ya ce wannnan ne ya sa suka ce ba su yarda ba sai an gyara, kuma al’ummar jihar Kano sun gane sun fahimta ana cigaba da tafiya tare da ba su goyon baya.

Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce yana fatan ‘yan jarida za su cigaba da yin abubuwa da za su haɓɓaka cigaban zaman lafiya da cigaban al’umma da matasa, kuma su cigaba da jajircewa a kan gaskiya, su jam’iyyar ta NNPP suna tare da dukkan mutane masu daraja da son ganin alheri da ba su da wani burin sai na don kawo cigaban al’umma.

Hon. Dungurawa ya ce suna tafiyar su ba sa tare da mutane masu son ta da fitina da ba su san darajar mutane ba don haka ‘yan jarida su zama daga masu bayar da gudunmawa wajen kawo zaman lafiya a jihar Kano da ƙasar nan baki ɗaya.

Tunda farko a jawabinsa sakataren Gidauniyar, Sulaiman Ahmad ya ce an zaɓi bai wa Hon. Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa shugaban NNPP na jihar Kano, wannan karramawa ne a matsayinsa na jagora da ke jajircewa a kan shugabanci na jam’iyya da yake ƙarfafa duk mai son cigaban jihar Kano.

Sun ƙara da cewa sun lura tun zaman sa shugaban jam’iyyar a ƙananan hukumomi 44 da kuma jihar sai ƙara haɓɓaka tasirin jam’iyyar yake duk da wasu da wasu ke kullawa jam’iyyar a jiha da ƙasa, amma irin jajircewar Dungurawa da koyi da yake da jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso jam’iyyar sai daɗa tasiri take.

Sulaiman Ahmad ya ce don haka Arewa Media Foundation and Development, wacce matattara ce ta ‘yan jarida da suke ƙoƙarin bunƙasa manufofin Arewa suka dubi irin jajircewa da tsayuwarsa a kan aƙida da gudunmawda da yake bayarwa ta karrama shi.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *