An Samu Fahimtar Juna Tsakanin Shugaban Ƙaramar Hukumar Rimin Gado Da Matasan Yankin

Daga
Ibrahim Muhammad

Gamayyar matasa masu kishin samar da cigaban ƙaramar hukumar Rimin Gado sun yi zama da Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Muhammad Sani Salisu Jili domin fahimtar juna da yadda za a ciyar da yankin gaba.

Wannan ya biyo bayan janye zanga-zangar lumana da matasan suka shirya yi kan matsalolin da ake fuskanta a yankin da suka haɗa da na matsalar ruwa da makarantu da asibitoci.

A yayin ganawar tasu, Shugaban ƙaramar hukumar na Rimin Gado, Hon. Jili ya ce, za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen samar da ruwa da kyautata makarantu da asibitoci don kyautata harkar ilimi da lafiyar al’ummar yankin.

Sani Salisu Jill ya ce, gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta amince da ɗaga likkafar asibitin Rimin Gado zuwa babba da faɗaɗa dam domin samar da wadataccen ruwan sha da inganta ɓangaren cigaban ilimi domin ko a kasafin kuɗi gwamnatin Kano ta fi ba ɓangaren ilimi fifiko.

Shi ma a nasa ɓangaren Shugaban matasan masu fafutukar kawo gyara da cigaban Rimin Gado, Salim Muhammad Mudassir ya ce sun zauna da shugaban ƙaramar hukumar sun sami daidaito da fahimtar juna, kuma za su ba su lokaci, kuma sun ce a je a kalli yadda yanayin asibiti, makarantu da samar da ruwa yake da kuma sanar da su tsare-tsaren da ake na gyara su.

Ya yaba da kyakkyawan haɗin kan da shugaban ƙaramar hukumar ya ba su. Ya shaida musu tsare-tsarensa, sun kuma ba shi shawarwari da suke fata nan da ɗan ƙanƙanin lokaci za a sami sauƙi a matsaloli da yake damun al’ummar yankin.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?