Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban ƙaramar hukumar Doguwa da ke jihar Kano, Hon. Abdulrashid Ridwan ya yi kira ga al’ummar yankin a kan da su zauna lafiya a tsakaninsu.
Ya yi kiran ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano, biyo bayan wata taƙaddama da faru a gonar Malam Salisu tsakaninsa da wani Bafulatani ɗan asalin jihar Kaduna mai suna Hore da hakan ta jawo rasa ran Malam Salisu a ranar 23/3/2025.
Dagacin Doguwa Alhaji Yusuf Umar kira ya yi da kwantar da hankali domin ƙaramar hukumar bisa jagorancin shugabanta Hon. Abdulrashid Ridwan na iya bakin ƙoƙari domin an samu zaman lafiya da kuma bin haƙƙin wanda aka kashe bisa adalci ta hanyar da doka ta tanada.
Ɗaya daga cikin shugabanin Muryar Al’ummar Doguwa Malam Suleman Rilwan, wanda ya wakilci shugaban ƙungiyar V.O.D ya bayyana irin ƙokarin da suka yi da matakan da suka bi wajen gano mai laifin wanda ya gudu zuwa garin Gani da ke a ƙaramar hukumar Sumaila, kuma tuni an ɗauki matakin shari’a a kansa.
Shi ma a jawabinsa, Aliyu wanda ɗa ne ga Marigayi Malam Salisu da aka kashe ya nemi gwamnati ta bi musu kadin sanadiyyar rasa ran mahaifin nasu, ya kuma roƙi mahukunta su yi musu adalci wajen hukunta mai laifin.






