Naɗin Galadima: Masarautar Kano Ta Sake Ɗaga Martabarta -Hon. Murtala Husaini

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar Kano da ma ƙasar nan gaba ɗaya shi ne mataki na nasara da jin daɗi a kowane yanayi.

Hon. Murtala Husaini S/gida Chiroman Sarkin Noman Gaya, kuma Wakilin Gonar Galadiman Kano, Kasilan Mazaɓar Balam ne, ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a taron naɗin sabbin sarautu da aka yi a fadar Kano.

Ya ce suna mutuƙar farin ciki da naɗin da aka yi na ɗaga likkafar Turakin Kano, Munir Sanusi ya zama Galadiman Kano, suna fata Allah ya taya shi riƙo.

Ya gode wa Sarkin Kano Muhammad Sanusi kan ƙoƙarinsa na haɗa kan masarautar.

Ya ce wannan taro na naɗin Galadima da sauran sarautu da mai martaba Muhammad Sanusi ya yi ya daɗa fito da kima da ƙoƙarin masarautar Kano na haɗa kan al’umma da inganta zaman lafiya da cigaba.

Hon. Murtala Hussaini S/gida ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su cigaba da bai wa gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano haɗin kai da goyon baya domin cin ma nasara a ƙoƙarin da suke na kare martabar al’umma da cigaban jihar.

  • Related Posts

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

    Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal