Daga Ibrahim Muhammad
Hajiya Hadiza Ali Bala, ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayi Galadiman Kano Abbas Sanusi da aka fi sani da Hajiyar Masallaci, kuma ake kiran ta da Sardaunan Mata ta bayyana naɗin da Sarkin Kano Muhammad Sanusi ya yi wa Yariman Kano daga gidansu abin farin ciki ne gare su zuriyar marigayi Galadiman Kano, Abbas Sanusi.
Ta bayyana hakan ne a yayin wata liyafar da aka shirya ta taya murna ga wasu daga waɗanda aka yi wa sabbin naɗe-naɗen mayan sarautu a fadar Kano.
Ta ce ta yi mutuƙar jin daɗin yadda ta ga al’umma suka zo daga sassa daban-daban daga ciki da wajen jihar Kano suka taya su murnan wannan naɗin da Sarkin ya yi a masarautar Kano.
Ta ce wannan naɗe-naɗen mukamai da aka yi duk sun shafe ta domin wanda aka bai wa Galadima a yanzu Baba Mannir Uba ne a gare ta. Hhaka wanda aka bai wa Wambai ɗan’uwnata ne, kuma ƙaninta. Haka shi ma wanda aka bai wa Yariman Kano Ahmad Abbas Sanusi, wanda suke kiran sa Ɗan Darman ƙaninta ne, kuma ɗanta.
Hajiya Hadiza Ali Bala Sardaunan Mata ta yi fatan dukkan waɗanda aka naɗa a muƙaman a masarautar Kano, Allah ya ba su ikon riƙewa da sauke nauyin da aka ɗora musu.






