Daga Ibrahim Muhammad
Sakamakon ƙorafe-ƙorafen al’umma da na ’yan kasuwa, Shugaban Hukuma KAROTA, Auwalu Lawan Shu’aibu Aranposu ya fita rangadin gani da ido da kansa, inda ya je mahaɗar WAPA da ke Kano, don ya gane wa idonsa yadda ake gudanar da harkokin a wajen, tare da jan kunnen masu ajiye motoci a kan hanya da masu kasa kaya a kan titi daura da ƙofar Fagge Upper Sharia Court da fakin ɗin motoci kan titin bayan kotun.
Kazalika, Shugaban Hukuma KAROTA ɗin ya leƙa Murtala Muhammad Way Kasuwar Singer har zuwa tsohuwar Bata, inda a nan ma ya samu masu kasa littattafai kan titin Bello Road da titin mai Ƙarami Plaza.
Wani abin takaici shi ne yadda mutane suka ajiye sikeli a kan titin Singa suna auna kwali da robobi da mata suna soya Awara da doya duk a kan titi, wanda hakan ba ƙaramin cutar da al’umma yake ba.
A ƙarshe Shugaban Hukuma KAROTA ya ja kunnensu, tare da gaya musu za fa a fito aiki don haka su gyara domin gwamnati ba ta son wulaƙanta kowa sai wanda ya wulaƙanta kansa domin gyaran in aka yi din al’umma za ta ji daɗi, in ji shi.






