An Shirya Wa Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda Mai Kula Da Kano Da Jigawa Faretin Bankwana Da Aikin Ɗan Sanda

Daga Ibrahim Muhammad

Shiyya ta ɗaya ta Mataimakin Sufeton ‘yan sanda na shiyya ta ɗaya mai kula da jihohin Kano da Jigawa ta gudanar da faretin bankwana ga Mataimakin Sufeton-Janar na ƙasa mai kula da shiyynar, AIG Ahmed Ammani Malumfashi sakamakon ritaya da ya yi.

Taron faretin bankwanan da ka gudanar a harabar hadikwatar shiyya ta ɗaya da ke Kano a yammacin ranar Juma’a, ya sami halartar manyan jami’an ‘yan sanda da suka haɗa da Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori PhD da na jihar Jigawa, A.T. Ahmed da sauran manyan jami’ai daga sassa daban-daban da ma waɗanda suka yi ritaya.

Da yake jawabin bankwana, Mataimakin Sufeton ‘yan sandan na ƙasa mai kula da shirya ta ɗaya, Ahmed Ammani ya gode wa abokan aikinsa manyan da ƙanana bisa irin haɗin kai da goyon baya da suka ba shi a sassa da matakai daban-daban da ya riƙe har zuwa wannan lokaci da ya gama aikin.

Ya kuma gode wa babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa Kayode Egbetokun bisa dama da ya ba shi, sannan ya yaba wa kwamishinonin ‘yan sanda na Kano da Jigawa da suka yi aiki a ƙarƙashin sa a wannan shiyya bisa irin haɗin kai da suka ba shi.

Ahmad Ammani ya yaba da irin haɗin kai da goyon baya da tallafi da gwamnonin jihohin Kano da Jigawa suka ba shi wajen samun nasarar kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Sannan ya yi addu’a da fatan alheri ga waɗanda yanzu suke aikin,
Allah ya sa su gama lafiya.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Kano da ya sami wakilcin Daraktan janar na ayyuka na musamman, AVM Ibrahim Umar mai ritaya, ya bayyana AIG Ahmad Ammani da cewa mutum ne jajirtacce da ya yi aiki tuƙuru da ya kamata a yi koyi da irin jagorancinsa a aikin ɗan sanda wajen nuna sadaukarwa.

A jawabinsu daban-daban, kwamishinonin ‘yan sanda na Kano; Ibrahim Adamu Bakori da takawaransa na Jigawa; Ahmad Tijjani Abdullahi sun yaba da irin kyakkyawawar alaƙa ta aiki da ke tsakaninsu da Ahmed Ammani, tare da taya shi murnar kammala aiki lafiya. Sun yi masa fatan alheri da kyakkyawan rayuwa.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun