Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana haƙuri a aure shi ne matakin da yakan sa ya ɗore a sami zaman lafiya, don haka yana da mutuƙar muhimmanci ma’aurata su karrama juna su rika mutunta iyayen juna da ba su daraja Allah zai musu Jagora ya sa albarka a auren.
Babban sakataren yaɗa labarai na Gwamnan jihar Kano, Mustapha Muhammad ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a ɗaurin auren ‘ya’yan mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam da aka yi a masallacin Alfurƙan ranar Lahadi.
Ya ce an san Mahaifin Amaren da aka ɗaura wa auren Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam mutum ne na jama’a mai karrama su da mutunta su. Don haka ba abin mamaki ba ne na ganin irin yawan mutane da suka zo don ɗaurin auren ‘ya’yansa.
Mustapha Muhammad ya yi nuni da cewa duk mutumin da yake karrama mutane suna duba mutuntawa da yake musu a dukkan sha’aninsa su je ballantana kuma shi mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam mutum ne karimi mai kyautatawa duk wanda ya zo kusa da shi.






