Manufarmu Kyautata Haɗa Kan Hausawa A Duniya -Dakta Muhammad Sa’id

Daga Ibrahim Muhammad

Gidauniya Hausa da haɗin kan Hausawan Duniya Charity ƙarƙashin jagorancin shugabanta na duniya, Dakta Muhammad Sa’id ta gudanar da taron bayar da muƙamai da shaida ga wasu daga mambobinsu.

Taron da aka gudanar a jihar Kano ya sami halartar ɗimbin mambobin Gidauniyar daga cikin da wajen ƙasar nan.

A yayin taron shugaban Gidauniya ya bayyana cewa wannan naɗe-naɗen da aka yi zai ƙara bunƙasa cigabansu.

Ya yi nuni da cewa Nijeriya ita ce cibiyar wannan ƙungiya, shi ya sa suka zaƙulo waɗannan jajirtattun mutane suka ƙara sa su a cikin ƙunshi na shugabancin Gidauniyar.

Dakta Muhammad Sa’id ya yi kira ga al’ummar Hausawa a faɗin duniya a kan su haɗa kai domin kawar da matsala da ake samu na rashin haɗin kai a tsakanin Hausawa shi ya sa suke wannan ƙoƙari ko’ina a duniya game da samun wannan haɗin kai da shi ne mataki na cigaba.

Dakta Muhammad Sa’id ya ce mutane biyar da aka bai wa shaidar muƙaman akwai na matsayin ƙo’odinata na Gidauniyar na duniya da kuma Tauraruwa ta Duniya da kuma Sakataren Janar na Gidauniyar na duniya da shugaban matasa na ƙasa.

Ya ce ana yin duba da dacewa da cancanta ne kafin a bayar da irin wannan matsayin sun bincika waɗanda suka sami muƙaman sun cancanta da matsayin, domin suna da kyakkyawan shaida a wajen jama’a.

Dakta Muhammad Sa’id ya ce Gidauniyar yanzu ta soma karɓuwa a ƙasar nan, ba kamar sauran ƙasashe da suka kafa reshensu ba da suka sami karɓuwa sosai, a nan Nijeriya, akwai ‘yan ƙalubale da ake fuskanta saboda akwai wasu ƙananan ƙungiyoyi da suke kallon wannan Gidauniyar ta Hausa da haɗin kan Hausawan Duniya Charity barazana ce a gare su, wanda kuma ba haka ba ne, suna gudanar da tafiyar da ita ne bisa sahalewar doka.

Shi ma Ko’odinata na Gidauniyar na Duniya, Alhaji Rabiu Muhammad Gumel ya ce, duk lokacin da za ka yi irin wannan Gidauniya da ta shafi duniya sai ka zauna ka ga su waye ma za su kasance a ciki, don sai ka sami jajirtattun mutane da za su tafiyar da ita, don haka akwai matakai da a kan bi don tantance mambobinta domin samun sahihanci da ingantattun mambobi jajirtattu da shugabanni ake sa wa.

Ya ce a matsayinsa na Ƙo’odinata na Gidauniyar na Duniya a halin yanzu da suke da wakilai a ƙasashen duniya 47 mafi yawan wakilansu da suke ƙasashen duniya mutane ne Hausawa ‘yan asalin ƙasashen wasu kasuwanci ne ya kai su da iyalansu suke zaune, sun zama ‘yan ƙasa suna da katin ɗan ƙasa da kuma mafi yawa wasu ma a can aka haife su.

Ya yi kira ga mambobin Gidauniyar su sani cewa wannan aiki ne suka ɗauko, wani abu ne na fafutuka domin irin wannan shi suka rasa a baya, yanzu lokaci ya yi da za a zaƙe damtse, yanzu an sami wata kafa ta samun wani jigo da za su riƙe a kai inda ba a tunanin a kai

Alhaji Rabiu Muhammad Adam Gumel
Jakadan Lautai Ƙo’odinata na Gidauniyar Hausa da haɗin kan Hausawan na Duniya ya ja hankalin masu ƙoƙarin su shigo tafiyar Gidauniyar su sani ana maraba da kowa, domin ta kowane Bahaushe ce da yake Duniya domin a had6u a gudu tare a tsira tare, kuma tasirinta Bahaushe bai taɓa samun wata Gidauniya irin wannan ba da ta tsaya ta kalli Bahaushe da kuma ina yake so ya je. Wannan tasa suna da tunanin harshen Hausa zai sami kujera ma nan gaba a Majalisar Ɗinkin Duniya. Wannan shi ne burinsu.

A yayin jawabinsa shi ma shugaban Gidauniyar Hausa da haɗin kan Hausawan Duniya reshen Nijeriya, Alhaji Shitu Adam Bargaja shugaban ƙungiyar Sakkwatawa da Kabawa da Zamfarawa mazauna jihohin Kano da Jigawa, ya bayyana farin cikinsa da taron da kuma kira ga mambobin Gidauniyar su dage wajen haɗa kan al’ummar Hausawa a duk inda suke domin tabbatar da kima da wanzuwar al’adunmu.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun