Ƙungiyoyin Kasuwar Singa, Kano Sun Jinjina Wa SIMDA Kan Aikin Gayyar Tsaftace Kasuwa

Daga Ibrahim Muhammad

‘Yan kasuwar Singa sun fito domin gudanar da aikin gayya don tsaftace kasuwar bisa umurnin da ƙungiya cigaban kasuwar da ake kira SIMDA ta bayar domin gyara magudanun ruwa don tsare kasuwar daga samun ambaliyar ruwa a daminar bana.

A yayin aikin, wanda Wakilin Kwamishinan kasuwanci na jihar Kano, Hon. Akibu Sarki Mahmud Gaya babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano a kan kasuwanci da zuba hannun jari ya halarta ya ce, sun shigo kasuwar sun ga aikin, sun ga yadda aka yi rumfuna kan magudanan ruwa, sun ji ƙorafin ‘yan kasuwa.

Ya yi nuni da cewa ba zai yiwu a ce an samu magudanan ruwa an yi rumfuna a kai ba. Gwamnatin Kano ba za ta lamunci wannan ba. Sannan sun yaba wa motsin ‘yan kasuwar Singa da suka fito ana wannan aiki da su wanda duk wajen cin abinci su ne suke gyarawa.

Aƙibu ya yi kira ga ‘yan kasuwannin jihar Kano su yi koyi da yadda ‘yan kasuwar Singa suka fito suke aiki da kansu ba Gwamnati ce take musu ba da irin wannan ƙoƙari gwamnati za ta shiga lamarin ta tallafa musu.

Shi ma mataimakin shugaban ƙungiyar cigaban kasuwar Singa SIMDA, Aminu Umar Dogara da yake magana a madadin shugaban ƙungiyar Batista Junaid Zakari Yusuf ya ce, tunanin aikin ya zo ne biyo bayan ambaliyar ruwa da ake samu a kasuwar a sakamakon toshewar magudanan ruwa.

Ya ƙara da cewa sai ƙungiyar SIMDA ta yi hoɓɓasa domin ta gudanar da aikin da hakan zai taimaka wajen kau da ambaliyar ruwa don kiyaye asarar dukiyoyi da yake aukuwa kusan duk shekara da damina a kasuwar.

Aƙibu ya ce, akwai matsalar da suke fuskanta na yin falitai a kan magudanan ruwa, suna ta ƙoƙarin samun daidatuwa da ƙaramar hukumar Fagge da sune ke ba da dama a yi irin wannan falitan a kan magudanan ruwa, kuma sun sha jan hankalin hukumomin ƙaramar hukumar su kaucewa ba da dama a yi, amma ba su amince ba, har yanzu suna kan tuntuɓar su a kai.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na SIMDA, Aminu Umar Dogara ya ce, wannan aikin da ‘yan kasuwar Singa suke da duniya ta gani, suna so al’umma su zama shaida, kuma gwamnati ta sani wannan falitai da ƙaramar hukumar Fagge ke sahalewa masu wuri ko a gaban gida ko kan magudanar ruwa ake yin faleti ba ƙaramin abu ne da yake kawowa wajen kasuwanci matsalar jawo ambaliyar ruwa ba .

Shi ma shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya na kasuwar
Singa, Alhaji Muntari Muhammad Liti Kwasangwami ya ce, suma sun fito aikin da sanyin safiya a kan titin Bello, kuma aikin na tafiya yadda ya kamata, tare da kira ga ‘yan kasuwa su ba da goyon baya domin samun nasarar aikin.

Ya taya alhazan jihar Kano murna da fatan an yi aikin Hajji karɓaɓɓiya, an gama lafiya tare da yi wa Gwamnan jihar Kano, injiniya Abba Kabir Yusuf fatan alkhairi da yaba masa a kan irin kulawa da ya bai wa alhazan jihar Kano a Ƙasa mai Tsarki.

Alhaji Kwasangwami ya yi fatan Allah ya ƙara wa jihar Kano da ƙasa baki ɗaya zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziƙin da cigaban kasuwanci a Kano.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal