GWAMNATIN JIHAR KADUNA NA KOKARIN WARWARE DA DADDEN MATSALAR RIGINGIMUN FILAYEN GARIN MAHUTA.

Al’ummar mahuta Dake kusa da national eye center a karamar Hukumar igabin ta jihar kaduna suna yabawa da salon jagoranci irin na maigirma Gwamnan jihar kaduna Sanata Dr UBA SANI CON.

Duba da Yanda kake kokarin Dawo da Martaban jihar ta kowane ɓangare musamman ma magance rigingimun Dake tsakanin masu Gonaki da filaye da dillalai a fadin jihar kaduna Wannan ya tabbatar Mana da cewa Gwamna UBA SANI Shugaba ne Adali me kaunar zaman lafiya, da cigaban jama’a, yanda ka Daura Alhakin warware matsalar a Hannun Hukumar KADGIS ta jihar kaduna.

To Saida wani Hanzari ba Gudu ba, ansami wasu masu yiwa wannan shiri naka kafar Angulu Domin yanda akace ayi ba Hakan akayi ba, saboda mune ainihin masu Wadannan Gonaki da muka GADA Daga iyaye da kakaninmu Kuma muke da shari’oi da ban da ban agaban ma banbanta kotuna, Kuma munada masaniyar cewa mune Wadanda kace azo a magance Mana damuwar mu, Amma Kuma cikin takaici sai gashi munaji Muna Gani ana Daukan CO4 ana rabawa ga wasu tsoffin sojoji da tsoffin Yan sandan da duk tare dasu muke shari’a a gaban kotuna, Wanda Kuma su basu da ko kafa Daya a wannan waje sun saya ne wajen inter Land Kamfanin da Shima muke gaban kotu tare dashi, sannan Kuma ita kanta Hukumar ta KADGIS din a yanzu haka Muna kan shari’a tare dasu a wata Kara da muka shigar Mai Lamba KDH/KAD/159/2015,
To sai Abin ya daure Mana Kai, wannan tasa muke tunanin cewa Director General na Hukumar KADGIS Bazai iya sasanta wannan matsalar ba, saboda ta bayyana karara Yana Dauka CO4 Yana mikawa ga mutanen da duk muke shari’a akan FILAYEN tare dasu a gaban kotuna Wanda haryanzu ba’a Gama shari’oin ba, mu Kuma yaki sauraranmu.
Sai dai Muna ZARGIN cewa Wasu Daga cikin sauran diddigan kayan Gwamnatin baya ne da Suka rage a Hukumar ta KADGIS suke kokarin lullubewa DG. KADGIS din Ido akan kada yayi Abinda kasashi yayi Saboda basa son Samun nasarar wannan GWAMNATI.
Amma Kuma Muna masu matuƙar Mika Godiyar mu da Jin Dadin yanda maigirma Director General na KASUPDA ya gudanar da nashi Aikin Kamar yanda Maigirma Gwamna ya umurta wannan ya tabbatar Mana dacewa mutum ne me son zaman Lafiya da cigaban Gwamnati da Al’umma Baki Daya.

Don haka Amatsayin mu na Yan kasa nagari masu biyayya da Dokokin Hukuma Kuma yayan jam’iyyar APC masu yiwa GWAMNA fatan Alkhairi, Muna Mika koken mu Ga maigirma Adalin Gwamna Wanda baisan zalunci da kayi gaggawan waiwayan wannan Lamarin Domin Maida komai bisa kan tsari Kamar yanda kabada umurnin cewa anememu A Kuma magance Mana matsalolin mu, DOMIN Samun dauwamammiyar zaman lafiya Aji har kaduna da kasa Baki Daya
ALLAH ya ja zamanin GWAMNA yaja zamanin jihar kaduna.

Rubutu: Kungiyar Ihsan Development Forum MAHUTA.

Related Posts

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara