Marigayi Aminu Ɗantata Ya Ba Da Gudunmawa Sosai Wajen Inganta Tsaro -AIG Garba Ahmad

Daga Ibrahim Muhammad

“Wannan babban rashi da muka yi na ƙasa baki ɗaya maye gurbinsa zai wahala. Marigayi Aminu Ɗantata mutumin kirki ne mai taimakon jama’a, in ji Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta ɗaya Kano da Jigawa, Garba Ahmad ne ya bayyana hakan da ya kai ziyarar ta’aziyya a gidan Marigayin.

Ya ce su a matsayinsu na ‘yan sanda masu kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba za su iya gane irin yawan gudunmawar da ya ba su ba a shekaru aru-aru. “Duk sanda aka samu damuwa a jihar Kano, wani sa’ in ma shi zai neme su ya nuna musu ga hanyar da za a bi a yi gaskiya da adalci a sami kwanciyar hankali.

AIG Garba Ahmad ya ce wannan ba sai lokacin wata tarzoma kaɗai ba, ko lokaci ma na siyasa ne yakan tsawatar, ya tabbatar da cewa sun tsaya kan ƙafafunsu sun yi aiki da adalci da gaskiya domin samar da zaman lafiya.

Ya ce Aminu Ɗantata ya yi amfani da dukiyarsa yana taimaka wa ma’aikatan tsaro ta fannoni daban-daban da ba da shawarwari da taimakawa gajiyayyu, talakawa abu ne da ba za a iya ƙididdige irin taimako da yake ba, sai dai a ce Allah ya jiƙansa ya gafarta masa, ya ba shi ladan aikin da ya yi.

Mataimakin babban Sufeto ‘yan sandan na ƙasa, ya shawarci mutane su gane cewa ita duniya ba matabbata ba ce, “Da mai arziƙi da talaka, tilas kowa sai ya tafi inda ake tafiya. Don haka masu dukiya su riƙa taimakawa talakawa, ma’aikata da gwamnati a riƙa tabbatar da ganin an sami cimma buri na zaman lafiya a wannan ɗan taƙaitaccen lokacin da kowa zai yi a duniya,” ya ƙarƙare.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History