Rashin Tallafin Gwamnati A Harkar Noman Kaji Na Kawo Mana Koma-Bayan -Dakta Jamilu Musa

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa rashin shigowar gwamnati cikin harkar kiwon kaji don ba da tallafi ga masu harkar yana sa wa harkar ta yi baya.

Dakta Jamilu Musa shugaban Kamfanin AB da AK Farm Agrovet Services ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a toron ƙaddamar da sabon abincin kaji da kamfanin TOPFEED suka gudanar.

Ya ce da gwamnati za ta shigo kamar irin sa da ya gama Jami’a tun shekaru shida da suka gabata bai taɓa aiki da gwamnati ba ga shi ya zama mai samar da aiki da a ce za ta tallafa wa ire-iren su wanda ya iya samar da aiki na mutum 10 zai iya sama wa 100.

Ya ce irin su ya kamata gwamnati ta shigo ta riƙa neman gudunmawa da shawarwari daga gare su domin su tallafa mata wajen samar da aikin yi ga matasa maza da mata kamar yadda gwamnati kaɗai ba za ta iya samar da aikin yi ba kowane matashi ya yi ƙoƙari ya dogara da kansa.

Ya ce yana da burin ganin matasa sun kama sana’a. “N daɗe ina gabatar da shirye-shirye a kafafen yaɗa labarai domin mu ga mun tallafa wa manoma sun ƙware, kuma sun samu wayewa a kan harkar kiwon nan. In gwamnati da mutane masu hali za su sa hannu, za a samu cigaba,” ya jaddada.

Dakta Jamilu Musa ya ce su ma manoman na haifar da nasu matsalolin na rashin neman shawarar masana a cikin harkokin kiwon nasu. “Ya kamata duk abin da manomi ya tashi zai yi a gona su nemo masana Kimiyyar dabbobi ko Likitan dabbobi ya duba ya ga me yake faruwa ga gonar ka”, in ji shi.

Ya ce wani lokaci tun wajen share gonar ake barin gini tun ran zane. Dole ka sami masani ya tsara maka ya za ka gina gonarka kajinka su zauna lafiya ba tare da matsala ba. “Waɗanan abubuwa ne da ya kamata manoma su yi amfani da su don amfani mai kyau,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ƙoƙari ne mai kyau da TOPFEED ta yi wajen samar da abincin kaji mai sauƙi da manoma za su iya saye da kuɗi kaɗan da za su iya samun abin da ya kamata na samar da ƙwai.

Dakta Jamilu Musa ya ce sun gwada abincin kajin yana da inganci da sauƙi da biyan buƙata da ya kamata sauran kamfanoni na samar da abinci su riƙa yin haka su ma.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History