Daga Ibrahim Muhammad
Ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Gazawa, Hon. Abdullahi Yahaya Tsakiyar Kara, Barden Gazawa a shekara biyu da ya yi na zuwan sa Majalisar dukokin jihar Kano babu daga mazaɓu da ke karamar hukumar guda 11 wacce ba ta amfani aikinsa ba.
Hon. Sani Muhammad Jogana mai bai wa ɗan majalisar jiha na Gezawa, Hon. Abdullahi Yahaya Tsakiya Karar shawara a kan harkokin ayyuka ne ya bayyana hakan.
Ya ce, “Muna da garin Dagaci 59 a ƙaramar hukumar Gazawa, duk mazaɓar da ka je ka ce ina aikin Hon. Abdullahi Yahaya Tsakiyar Kara za a nuna ma. A duk ‘yan majalisu na jihar Kano shi ne wanda ya naɗa masu ba shi shawara da suke ɗaukar albashi guda 37 da duk wata ake biyansu.”
Ya ƙara da cewa shi ne kuma ɗan majalisar da bai barin gidansu na gado ba ya tare a wani wuri, tun ma yana shugaban ƙaramar hukumar Gazawa a gidansu yake a garin su na Tsakiyar Kara. “Duk muƙamai da ya hau, daga kan zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukuma, har ya sake yin na riko, ya sake zama zaɓaɓɓe karo na biyu
a gidansu za ka same shi, sai dai in wani uzuri ya fitar da shi na aiki” in ji shi.
Hon. Sani ya ce, “Duk masu yin ƙorafi na adawa ta siyasa cewa ba su ga abin da yake ba, sune wanda suka dogara Barde ne zai musu komai ba Allah ba. Shi kuma ɗan majalisar na jiha na Gezawa ba zai iya abin da Allah zai yi ba, yana yin iyakar iyawarsa ne a matsayinsa na ɗan”adam da Allah ya ba shi iko.
“In aka yi la’akari da ɗan majalisar jiha na Gazawa na baya wanda jama’a suka sauke a lokacin zaɓe, shekara 16 yana wakilci a majalisar jiha har Kakakin majalisar Kano ya riƙe, amma in ka ce ina magudanan ruwa da rijiyar burtsatse da ya yi wa al’ummar Gezawa ba za a iya nuna maka su ba,” Hon. Jogana ya tabbatar.
Mai bai wa ɗan majalisar jiha na ƙaramar hukumar Gezawa shawara ya ce, shi kan sa misali ne na irin ayyukan Barde a Gezawa domin a lokacin da ya gama makarantar ƙaramar sakandare, iyayensa masu ƙaramin karfi ne, ba su da damar ɗaukar nauyinsa ya cigaba da babbar Sakandare. “Amma lokacin ɗan majalisar na yanzu shi ne shugaban ƙaramar hukumar Gazawa ya zo garin Jogana ya fara gina rukunin ajujuwa na babbar makarantar Sakandire, a nan na samu dama na cigaba da karatu na gama har na sami damar zuwa Jami’a,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa ɗan majalisar jiha na Gezawa, burinsa kyakkyawa ne, ba kawai ga ‘yan ƙaramar hukumar Gazawa ba har ma da jihar Kano gaba ɗaya, kuma cikin shekaru biyu a majalisa abin da ya yi da suke alfahari da su ba za su ƙirgu ba, don mutum ne da yake gina cigaban rayuwar al’umma ta ba su tallafi ya raba babura da yawa da ba da jari, yanzu ma yana tanadin ƙara tallafa wa al’umma da babura da kekunan ɗinki da injunan taliya da na markaɗe da mata da matasa da sauran al’umma a ƙaramar hukumar daidai gwargwado.
Hon. Sani Muhammad Jogana ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Gazawa su kalli damar da Allah ya bai wa Barden Gazawa na zama Wakilinsu a majalisar jiha wanda a Kano ta Tsakiya gaba ɗaya su biyu ne ‘yan majalisa da aka zaɓa a jam’iyyar APC na Gazawa da na Warawa, shi na Warawa ya yi ɗan majalisa sau huɗu, amma nasu na Gazawa zuwan sa na farko ke nan.
Hon. Sani Muhammad Jogana ya ce amma shekaru biyu da Barde ya yi da zuwan sa majalisa kusan ya fi wanda ya je majalisar jiha na Gezawa ba baya da ya je sau da dama yin abin da al’umma ke yabawa. Sannan kullum Hon. Abdullahin Yahaya Tsakiya Kara yana zuwa ziyarar dubiyar marasa lafiya da jaje da ɗaurin aure da ta’aziyya. “Wannan ya nuna kashi 90 na al’ummar Gezawa sun aminta da shi, kuma ba su yi zaɓen tumun dare ba suna kuma alfahari da wakilcinsa,” Hon. Jogana ya jadadda.








