Sun karrama Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da lambar yabo

A ranar Asabar 13 ga watan Satumban 2025 makusantan tsohon shugaban jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma ta jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi sun gudanar da gagarumin taron murna da farin cikin kammala aiki lafiya tare da karrama shugaban rukunin jami’oin Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da lamar yabo.

Gagarumin bikin wanda aka gudanar da shi a babban ɗakin taro na kwalejin ilimi na Tarayya (FCE) Bichi ya samu halartar ɗimbin masoya daga ko’ina a faɗin Nijeriya.

Farfesa Abubakar Adamu Rasheed tsohon shugaban Hukumar dake kula da jami’oin ƙasa (NUC), a yayin da yake jawabi ya bayyana Farfesa Armaya’u a matsayin mutumin kirki mai tausayi da ƙaunar jama’a.

Ya ƙara da cewa ‘yan’uwa da abokan arziƙi da suka shirya wannan biki na karrama Farfesa Armaya’u Bichi tare da bashi lambar yabo tare da wasu muhimman mutane waɗanda suka taimaimake shi wajen gudanar da shugabanci sun kyauta sannan sun ajiye ƙwarya a gurbinta.

Shima da yake gabatar da jawabinsa, shugaban riƙo na jami’ar gwamnatin Tarayya dake Katsina (FUDMA), Farfesa Aminu Ado ya ce Bichi mutum ne mai jin tausayin al’umma musamman mutanen dake ƙarƙashinsa.

Farfesa Ado ya ce har ƙasa ta naɗe ba zai mance da irin gagarumin ci gaban da Farfesa Arma’yau ya kawo ma jami’ar FUDMA ba.

Haka kuma a yayin bikin an ƙaddamar da littafin waƙoƙin da wasu mawaƙa suka yi wa tsohon shugaban na FUDMA mai suna ‘MALAMI A BAKIN MAWAƘA,’ wanda wasu ma’aikatan jami’ar suka rubuta.

Babban mai ƙaddamar da littafin, kuma shugaban ƙungiyar Jami’oin Afrika masu zaman kansu, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda ya samu wakilcin Dakta Ali Yusuf Kakaki ya sa ya sayi kwafi biyu a kan naira miliyan biyu (N2, 000, 000), sai kuma Sanata Alu Magatakardan Wamako ya sayi kwafi uku kan naira miliyan ɗaya.

Frafesa Armaya’u Bichi, ya nuna godiyarsa ga waɗanda suka shirya wannan taron domin taya shi murnar kammala aiki lafiya. Tare da jinjina da fatan alheri ga kafatanin waɗanda suka samu damar halartar wannan taro.

A yayin taron An karrama Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da shi kansa Farfesa Armaya’u Bichi da Farfesa Abubakar Rasheed da Malam Rufa’i Bichi da Malam Adamu Adamu, tsohon ministan ilimi a zamanin mulkin Buhari.

Related Posts

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun