Daga Ibrahim Muhammad
An buɗe masallacin ’yan nama da ke harabar Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi (Kasuwar Sabon Gari), wanda ƙungiyar mahauta ta sabunta gininsa, tare da mayar da shi na zamani.
Babban Malami, Sheikh Ibrahim Khalil ne ya jagoranci Sallar Azahar a masallacin, tare da bayyana aikin a matsayin aiki na alheri, inda ya ja hankalin al’umma kan tsaftar masallaci, tare da yin alƙawarin bayar da gudunmawar Naira 50,000.
Manajan Daraktan Hukumar kasuwar, Hon. Abdul Bashir Hussaini, ya bayyana masallaci a matsayin gidan Allah, yana mai jaddada cewa duk wanda ya taimaka wajen gina shi zai samu lada mai yawa.
Ya kuma yaba wa ƙungiyar mahauta bisa haɗin kai da rawar da suka taka.
Tsohon shugaban hukumar kasuwar, Alhaji Sa’id Dattijo Adahama, da shugabannin ƙungiyar mahauta sun bayyana farin cikinsu kan sabunta masallacin da aka gina shekaru da dama da suka gabata.
Mai zanen ginin masallacin, Arc. Binta Ahmad, ta yaba da haɗin kai da biyayyar ’yan nama, tare da bayyana shirin ɗora bene domin ƙara faɗaɗa masallacin a nan gaba.
Shugabanni da ’ya’yan ƙungiyar mahauta sun gode wa Hukumar kasuwa da ɗaiɗaikun mutane bisa gudunmawar da suka bayar, suna mai tabbatar da aniyar cigaba da inganta masallacin domin amfanin al’umma.





