Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

Daga Ibrahim Muhammad

An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma.

Wannan kira ya fito ne daga Arc. Binta Ahmad Umar, Darakta a sashen Park and Recreation Centre na KNUPDA, yayin wata tattaunawa da ’yan jarida.

Ta ja hankalin mata da su kwantar da hankalinsu, tana mai jaddada cewa aikin Architecture ba ya gagararsu. Ta ce, da yardar Allah, idan suka shiga fannin za su iya yin nasara, don haka ya dace su daina jin tsoro ko ja da baya wajen karatun.

Ta ƙara da cewa, duk da cewa akwai wasu ɓangarori a fannin da mata suka fi dacewa su shiga, ƙarancin mata a ciki na iya kawo gibi. Saboda haka, ta ƙarfafa mata da su dage kamar yadda ake yi a kowane irin fanni na ilimi.

A cewarta, babban bambanci tsakanin Architecture da wasu fannoni shi ne yana ɗaukar lokaci da ƙwazo, wani lokaci mutum na iya kwana yana yini yana zane.

Sai dai ta jaddada cewa, cikin ikon Allah, mutum zai so aikin har ya fi masa komai, domin abin da ake buƙata shi ne jajircewa da sadaukar da lokaci.

Arc. Binta Ahmad Umar ta bayyana irin gogewarta a fannin, inda ta ce ta yi ayyukan zane-zane da dama, ciki har da gine-ginen gidaje.

Ta taɓa aiki a Hukumar Ilimi ta Bai-ɗaya (SUBEB) a sashen Physical Planning, kuma tana alfahari da zagayawa dukkan ƙananan hukumomin Kano domin duba ayyukan ajujuwa, banɗakuna da sauran gine-ginen makarantu.

Ta ƙara da cewa, zaman aikinta a SUBEB ya ƙara mata ƙwarewa da gogewa, domin aiki kai tsaye ne ke ƙarfafa basira a Architecture.

A ƙarshe, Arc. Binta Ahmad Umar, wacce ta taɓa rike muƙamin Darakta na Fasaha a kasuwannin Muhammad Abubakar Rimi da Singa, ta bayyana cewa a da, lokacin da suke karatu, mata kaɗan ne a fannin Architecture, amma a yau abubuwa na sauyawa, domin ana fara samun mata da yawa masu sha’awar karatun fannin.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Daga Ibrahim Muhammad An buɗe masallacin ’yan nama da ke harabar Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi (Kasuwar Sabon Gari), wanda ƙungiyar mahauta ta sabunta gininsa, tare da mayar da shi na…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History