Ba A Sace Mutum 500 Ba A Zamfara -Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar tsaro ta ƙasar nan (DHQ) ta bayyana cewa tana samun gagarumar nasara a yaƙin da ta ke yi da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, inda kuma ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa, cewa wai an sace mutum 500 a Ƙaramar Hukumar Zurmi ta jihar, ta ce, wannan ƙarya ce tsagwaron ta, wacce wasu maƙiya zaman lafiyar jihar ke yaɗawa.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan jiya Juma’a a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya ce a zahiri an sace mutane huɗu ne kawai, saɓanin alƙalumman da ake yaɗawa.

Janar Buba ya jaddada cewa dakarun Operation Hadarin Daji suna aiki ne a cikin wani yanayi mai cike da ƙalubale, inda ya zama dole su magance haƙiƙanin gaskiya da kuma bayanan ɓata-gari, musamman daga shafukan sada zumunta.

Ya ƙara da cewa, maganar mutane 500 da aka yi garkuwa da su, wani ƙarin gishiri ne, inda aka tabbatar da sace mutane huɗu ne kawai.

Buba ya kuma ba da tabbacin cewa sojojin za su ci gaba da mai da hankali wajen fatattakar ‘yan ta’adda, inda tuni aka kawar da shugabannin ‘yan ta’adda da dama.

Haka zalika ya ce, sojoji na haɗa kai da jami’an tsaro da al’ummar jihar Zamfara domin inganta tsaro, duk da ƙalubalen da ake fuskanta, domin cikin taimakon Allah, sojoji na da ƙarfin faɗa da ‘yan ta’adda, inda suke samun nasarori a ayyukansu.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Daga Ibrahim Muhammad An yi kira ga mata da su ƙara jajircewa wajen karatun fannin zayyana gine-gine (Architecture) domin bayar da gudunmawa ga bunƙasa cigaban al’umma. Wannan kira ya fito…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History