Mutane fiye da dubu 6 ne suka amfana da tallafin Asusun Abba Aliyu daga sassan daban daban na birnin Kano.
Bukin rabon tagomashin wanda ya gudana asabar din nan ya shafi mata da matasa da dattawa da sauran marasa galihu dake cikin al’umma.
Asusun wanda Shuguban hukumar samar da Lantarki a Karkara ta kasa Dr Abba Aliyu Abubakar ya asasa ya sami wakilci Malam Sulaiman Aliyu Abubakar, yace zuwa yanzu Asusun ya horas da matasa sana’o’in dogaro da kai iri daban daban.
Bugu da kari Asusun Abba Aliyu ya kuma gwangwace wadannan da suka anfana da shirin da kayayyakin koyon sana’o’in yace kawo I da tallafin jari da kudaden more rayuwa.
Banda wannan ma, wasu mutanen dubu biyar sun sami tallafin kudade kamar yadda shugaban wannan Asusun, Kogunan Kasar Hausa Alhaju Dau Aliyu ya yi bayani tare da kira ga al’umma da masu hannu da shuni su yi koyi da wannan bawan Allah Abba Aliyu Abubakar wajen tallafawa al’ummar da suke zauna a cikin su don rage musu irin matsalolin rayuwa da suke fama da ita.






