Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana cewa a dukkan Nijeriya idan aka ce wane ne Gwamnan ma’aikata, ba kawai ma’aikatan jihar Kano na faɗin ƙasar nan ma, za su ce Abba Kabir Yusuf ne.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi na ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Muhammad ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya ce duk abin da Gwamnan jihar Kano zai yi domin jin daɗin ma’aikata tun daga zuwan sa yana yi, musamman a mataikin jiha da na ƙananan hukumomi ya zo yana biyan basusukan na fansho da ya zo ya tarar ba a biya ba.
Ya yi nuni da cewa su a ƙananan hukumomin da sauran ma’aikata daga ranar da aka ce an yi ƙarin albashi na N70 ,000 shi Gwamna Abba Kabir Yusuf bai tsaya a haka ba, sai da ya ƙara ma a kai, kuma ya biya a kan lokaci ba tare da wata matsala ba.
Ya ce su abin da yake ci masu tuwo a ƙwarya shi ne na Hukumar ma’aikata na ƙananan hukumomi, kuma yanzu Gwamna ya faɗa ya yi Hukumar nan, ya samar mata da wuri wanda za ta fara aiki. Kuma yana sahalewa ma’aikata bukatunsu.
Kwamared Ibrahim Muhammad ya ce ƙungiyarsu ta NULGE mai son cigaba ce, duk abin da zai kawo mata nasara a cikin al’amuranta shi suka sa a gaba. Shi ya sa suke samun nasara na samun kofi a taron ranar ma’aikata, shi ya sa ma sun ɗauki kofi a taron bukin ranar ma’aikata ta duniya, kuma za su cigaba da ɗauka a gaba.








