Abin Da Ya Sa Hafsat Ta Kashe Nafi’u

 

Wata matar aure mai suna Hafsat Surajo ta bayyana yadda ta kashe wani saurayi da yake masu aikace-aikace a gida, Nafi’u Hafiz, bayan ya hana ta kashe kanta.
Hafsat, wacce ta bayyana hakan a lokacin da aka gabatar da ita a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan Kano, ta ce mumunan lamarin da ya kai ga mutuwar Nafiu, ya faru ne a lokacin da rikici ya barke a tsakaninsu inda ya hana ta cimma burinta.
A cewarta, “Na kashe shi ne saboda ya hana ni kashe kaina. Yayin da ya yi yunkurin kwace wukar daga hannuna, sai rikici ya barke a tsakaninmu, kuma ana cikin haka sai na yanke a hannuna, sai jini ya rika fita.
“Ya ce in shiga in canza kaya. Bayan na fito sai na gan shi a kwance a kan kujera. Na ga wukar (da na kashe) a gefensa, sai na yi amfani da damar na dauko wukar na caka masa a wurare da dama.”  Hafsat ta bayyana.
Sai dai wata majiya ta shaida mana cewa akwai alakar kasuwanci mai karfin gaske tsakanin Hafsat da Nafi’u, abin da ya sa ya baro inda yake da zama ya dawo gidanta.
Kwamishinan ‘yan sanda, Mohammed Usaini Gumel ya tabbatar da faruwa lamarin, tare da kama mijin Hafsat, Dayyabu Abdullahi da mai gadinsu, Malam Adam bisa zargin hada baki da boye gawar marigayin.
A cewarsa, “A ranar 21/12/2023 da misalin karfe 0700 na safe, mun samu rahoto daga wani da ake kira Hafizu Salisu da ke zaune a cikin garin Bauchi cewa, ya samu kiran waya daga wani Dayyabu Abdullahi da ke zaune a Unguwa Uku, Kano cewa dan’uwansa Nafi’u Hafiz mai shekaru 38, ya rasu, kuma su zo su kai gawar don binne gawar.
“A lokacin da suka isa gidan da ke Unguwa Uku Kano, sun gano raunuka da dama a sassa daban-daban na gawar dan’uwan nasu da ake zargin kashe shi aka yi ba mutuwa ce ta Allah da Annabi ba.
“Likitoci a asibitin koyarwa na Aminu Kano sun tabbatar da mutuwarsa. Bincike ya kai ga kama Hasfat Surajo, mai shekaru 24, matar aure a gidan da marigayin ke zaune,” in ji
Bayan binciken da aka yi a sashin binciken manyan laifuka na rundunar, Hafsat ta yi ikirarin ita kadai ta aikata wannan aika-aika ta hanyar daba wa marigayin wuka a sassa da dama na jikinsa a lokacin da yake kokarin hana ta kashe kanta.
Kwamishinan ‘yan sandan, CP Gumel ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.

Related Posts

Bincike Ya Tabbatar Ƙungiyar Da Ta Zargi Gwamna Lawal Da Yi Wa ’Yan Bindiga Afuwa Ta Bogi Ce

An gano cewa zargin da ake yaɗawa cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi afuwa tare da sakin ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci ba shi da tushe…

Gidauniyar Abba Aliyu Gandu Ta Raba Solar Ga Al’umma

Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal