Daga Ibrahim Muhammad
Jam’iyyar ADC mai alamar musabaha reshen jihar Kano ta gudanar da taron gangamin na ƙoƙarin haɗa kan jam’iyyu domin yadda za a haɗu waje guda don a tunkari jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa.
Taron da ya sami halartar dukkanin musu ruwa da tsakin jam’iyyar ADC na jihar da wakilan wasu jam’iyyu da suka haɗa da PDP da PRP da sauran wasu jam’iyyun da kuma wasu malaman Jami’a suka gabatar da jawabai a kan abin da ya shafi haɗin kai.
A yayin taron da ya gudana a ɗakin taro na Gidan Mumbayya, tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023.
Malam Ibrahim Khalil ba jawabinsa ya bayyana jam’iyyar ADC ita ce tamkar jirgin Annabi Nuhu ga ƙasar nan don ta sha bamban da dukkan sauran jam’iyyu domin akwai adalci da kuma ɗan’adam a cikinta da bai wa kowane mutum haƙƙinsa.
Ya ce a jam’iyyar ADC. iyaye mata da mutane masu buƙatar ta musamman ba za su sayi fom ba, kyauta za a ba su a dukkan takara da za su nema su tsaya, sannan su ma matasa da ba su kai shekaru 40 ba, kyauta za a ba su fim. “Wannan kaɗai ya bambanta ADC da duk wata jam’iyya da take a ƙasar nan,” in ji shugabannin jam’iyyar.
Sheikh Ibrahim Khalil ya ce jam’iyyar ADC ita ce wacce za ta karɓi kowa da irin halinsa, sannan kowa zai sami abin da ya dace da shi ba tare da an zalunce shi ba, kuma shi ba zai sami damar ha’inci ba, kuma wanda za a tunkara yanzu sai an tashi an yi yaƙi sosai a kanta, domin ita jam’iyyar APC kamar balam- balam ce wacce idan kana hurawa in ta cika sai ta fashe, haka za ta fashe ko a kan rikicin takara ko idan an kayar da su su yi rigama.
Shi ma wanda ya yi takarar mataimakin Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADC, Dakta Aminu Anas Abdurrahman ya ce sun gode wa Allah da ya ba su damar gudanar da taron cikin nasara kowa ya san an shaƙe ƙasar nan. “Muhimmin abu shi ne kula da zaman lafiyar al’umma da dukiyarsu da kare rayuwarsu,” in ji Dakta Abdurrahman.
Ya ce ƙasar nan gaba ɗaya ana ganin irin abin da yake faruwa ana shugabanci da babu alƙibla, babu damuwa da mene ne ke faruwa ga mutanen ƙasa, ba yadda za a yi kana shugabancin mutane, abin da ya dami mutane ba shi ne ya dame su ba. “Duk fariyar wannan gwamnati na cewa ana tara kuɗi ne wanda ba shi ne tsarin tattalin arziƙi ba.
“Tsarin tattalin arziƙi shi ne ka sauko ka yi tunanin mene ne zai zama rufin asirin al’ummarka, mutane kada su riƙa zama cikin fargaba da zulumi, wanda ake ciki yanzu a kusan dukkan ƙasar nan, musamman ma a Arewa da ake a cikin fargabar tsaro.”
Dakta Aminu Anas Abdurrahman ya ce wannan haɗaka da za a yi a jam’iyyarsu ta ADC an yi kira sun amsa, kuma suna roƙon Allah ya dafa musu, wanda duk suka zo suka ce sun yarda da tafiyar Allah ya sa da yaƙinin gaskiya suke yi.
Shi ma shugaban jam’iyyar na ADC na jihar Kano, Hon Musa Ungogo ya ce taron na ganganko ne da ake so a haɗa don ceto ‘yan ƙasa da suka shiga mawuyacin hali sanadiyyar gwamnatin APC, wanda sai lallai an haɗa kai an kawar da wannan gwamnati da suke abin da suka ga dama.
Ungogo ya ce ya zama wajibi su taimaki al’ummar ƙasar nan domin duk a jam’iyyun ƙasar nan ADC ce ba ta da rigima, ba ta da wata shari’a a kotu, tsarkakakkiyar jam’iiyya ce ba kamar sauran jam’iyyu ba da ake ta raba kansu. “Don haka duk masu kishi za su baro jam’iyyarsu su dawo a yi gangami na runduna masu gaskiya da amana a ADC a karɓi ƙasar nan a ceci al’ummarta,” in ji shi.







