Daga Ibrahim Muhammad
“Wannan rashi da aka yi na Alhaji Aminu Ɗantata rashi ne babba na Uba, shugaba abin alfahari gare mu ba rashi ba ne da jihar Kano ta rasa har ma ƙasa baki ɗaya har ma al’ummar Musulmi na duniya. Wannan rashi ya shafe su gaba ɗaya Allah ya gafarta masa ya ba shi Aljanna.”
Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar birnin Kano, Hon. Abubakar Nuhu Ɗanburan ne ya bayyana hakan.
Ya ce Alhaji Aminu Ɗantata shi ne irin mutumin da ake cewa Allah ya yi masa arziƙi da kowa zai yi fata ya yi koyi da irin abubuwan da ya yi na rayuwa a duniya.
Arziƙinsa da wadatarsa sun yi amfani ba wai kawai ga iyalansa, jikokinsa ko surukansa ba, har al’umma da ‘yan’uwa da abokan arziƙi da kuma al’ummar Musulmi na duniya.
Ya ƙara da cewa domin ya amfanar da abubuwa da yawa ya taimaka sosai, wasu abubuwa ma da ya yi ba a sani ba sai yanzu ne wasu suke ta fitowa. “Ya yi hidima tsakaninsa da Allah. Ɗaya daga cikin sakamako da wannan abubuwa suka haifar masa shi ne na yadda aka yi jana’izarsa a Madina, aka binne shi kusa da Annabi (saw). Wannan ba ƙaramar daraja ba ce. Allah ya nuna masa tun daga duniya,” inji shi.
Ya ce, “Domin a matsayin Aminu Ɗantata na bakin fata ɗan Nijeriya ba a taɓa samun wani baƙar fata a duniya ya rasu a wata ƙasa ba, kuma a ba da damar a ɗauko shi a sahale masa a yi jana’izarsa a Birnin Madina, masallacin Manzon Allah. Sannan a binne shi a kusa da Sahabbai da aka binne a wajen. Rayuwarsa ta yi kyau, sai godiya ga Allah. Muna fata Allah ya saka masa da Aljanna.”
Hon. Abubakar Nuhu Ɗanburan ya ce ba zai taɓa mantawa ba haduwar su da Alhaji Aminu Ɗantata ta ƙarshe ita ce ranar ƙaramar Sallah ya je wajensa a Makka bayan an kammala Azumi a nan ya yi Sallar Idi, shi kuma Allah ya kai shi Makka a wannan lokacin. Dama duk shekara yakan kai masa ziyara ya gaishe shi. Wani abin ban sha’awa a rayuwarsa, duk da yawan shekaru Allah bai sa ba ya gane jama’a ba da kuma lafiyar yin magana ga mutane har ya yi barkwanci.
Ya ƙara da cewa har sai da kamar yadda ya ga ‘ya’ya da jikoki suke ta ɗaukar hoto da shi. “Na ce da shi ni ma ina so a ɗauki hoto da ni. Sai ya ce to kar in yi fasta da shi. Na ce to ai in na yi fasta da shi ai gado na yi, domin shi ma ya taɓa yin ɗan majalisa mai wakiltar Kura a 1960. Saboda haka na ce ai in na yi, koyi na yi da kai. Ya yi dariya muka ɗauki hoto.
Hon. Abubakar Nuhu Ɗanburan ya ce baiwar da Allah ya bai wa Aminu Ɗantata na riƙewa da gane jama’a a tsawo shekaru sama da 90 ba ƙaramar baiwa ba ce. “Sai dai kullum abin da yake faɗa mana shi ne ‘ku saka haƙuri a rayuwa, ku zama mutane masu riƙe amana da gaskiya. d
Duk abin da za mu yi, mu yi don Allah. Mu tsaya mu taimaka wa addininmu.’ Allah ya ba mu ikon samun mutum irin sa da muka kasance da shi muka koyi abubuwa da yawa na halayensa masu kyau,” ta tabbatar.






