Al’umma Su Dage Da Yi Wa Ƙasa Addu’a Kan Halin Tsanani Da Ake Ciki -Hon. Aqibu Sani Nabayye

Daga Ibrahim Muhammad

An yi kira ga al’umma su dage wajen cigaba da yi wa ƙasar nan addu’a a wannan sabuwar shekarar Musulunci da muka shiga a kan Allah ya ba ta shugabanni na gari domin an riga an faɗa rami gaba dubu, rayuwa ta yi tsananin tsada, matsaloli kowa ya shiga ciki a dage da neman taimako da jinƙan Ubangiji ya bai wa ƙasa zaman lafiya da cigaba mai albarka da alkhari.

Hon. Aqibu Sani Nabayye tsohon ɗan takarar majalisar tarayya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Fagge a zaɓen 2023 ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen taron walimar ɗalibai da suka yi saukar Ƙur’ani na makarantar Thimaru.

Hon. Aqibu Nabayye wanda shi ma tsohon ɗalibi ne a makarantar da yake ba da gudunmawa ga cigabanta ya ja hankalin ɗalibai da suka yi saukar Alƙur’ani na makarantar su dage wajen cigaba da tilawar Ƙur’anin bayan wannan sauka da suka yi, su kuma karantar da shi. Domin Annabi (swa) ya ce mafi alkhairi daga cikinku shi ne wanda ya karanci Alƙur’ani, kuma yake karantar da shi.

Ya ce ya kamata iyayen yara da malamai su guji ɗoruwa a kan masu mulki ko ‘yan siyasa domin gudanar da irin waɗannan makarantu, su kyautata tsarin yadda za su riƙa tafiyar da makarantar ba sai an nemi taimako daga wasu ba, iyaye su zama sune ƙashin bayan kulawa da makarantun.

Sannan ya yi kira ga masu gudanar da makarantar su guji dogaro da ‘yan siyasa wajen neman tallafin tafiyar da makarantar domin an riga an sani su ‘yan siyasa idan ba sa a aka yi ba, mutane ne masu wahalar sha’ani, lokacin da za a zo, kalmar da ya kamata a yi wa mutum saboda ya zo a matsayin wakilin makaranta, ana so ya taimaka mutum ya yi aiki a makarantar da ‘ya’yan talakawa da yake mulka ko wakilta suke da lalura a ciki, amma sai ya ɗauki wannan mutumin a matsayin bara ko maula ya zo ko a kan buƙatar kan sa.

Hon. Aqibu Sani Nabayye, wanda a taron yana daga waɗanda suke bayar da tallafin kuɗi ga makarantar, ya ce, duk abin da za a nema don yi wa makarantar hidima, bai wuce abin da iyayen yaran za su iya yi ba. Don haka ba komai ne ya kamata a ce an tafi roƙon wani ya yi ba don ko a shari’a ba a yarda wani ya roƙi wani abu ba, ko da abinci ne sai idan ba shi da abincin da zai ci yau, duk me abin da zai ci yau da gobe ba a yarda ya yi roƙo ba. In aka yi kyakkyawan tsari iyaye za su iya tafiyar da makarantar.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?