Al’ummar Kano Su Fito Su Yi Rijistar Katin Zaɓe Don Tabbatar Da Nasarar Abba da Kwankwaso A 2027 -Mariya Ali Zage

Daga Ibrahim Muhammad

An yi kira ga ‘yan Kwankwasiyya da sauran al’ummar ƙasar nan a duk inda suke su tabbatar sun yi rijistar katin zaɓe domin tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan jihar Kano karo na biyu da zaɓar Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da yardar Allah.

Hajiya Mariya Ali Zage, shugabar matan Kwankwasiyya (woman Leader) ta Saudi Arebiya, kuma mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, Hon. Salim Hashim shawara a kan kasuwanci da saka hannun jari ce ta yi kiran.

Ta ce al’ummar jihar shaida ce na irin ɗimbin aikace-aikace da Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf da sauran zaɓaɓɓu ‘yan jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya suke ta aiwatarwa a lungu da saƙo ta tallafa wa mata da matasa da inganta samar da ruwan sha da gina hanyoyi da inganta harkar ilimi, ana gyaran makarantu ana kai ɗalibai karatu har ƙasashen waje.

Hajiya Mariya Ali Zage ta yi nuni da cewa saboda haka abu ne mai kyau mutane su fito su yi rijistar katin zaɓe, wanda bai taɓa yi ba ya yi, wanda nasa ya ɓata ya sabunta, wanda kuma shekarunsa ya kai ya yi, domin hakan zai ba da damar cigaba da amfanar muhimman ayyuka da da gwamnatin jihar Kano take a tsarin tafiyarsu ta Kwankwasiyya.

Ta yaba da yadda ta ga mutane na ta zuwa suna yin rijistar katin zaɓen, tun daga soma shi. Don haka ita ma a matsayin ta shugabar mata ta Kwankwasiyya ta Saudi Arebiya a ƙaramar hukumar Birnin Kano da wasu ƙananan hukumomi na ƙwaryar Birni Kano take ba da gudunmawa na tallafa wa mata da matasa domin su je su yi rijistar katin zaɓen, domin shi ne makamin da za su yi zaɓe da shi na tabbatar da nasarar Abba da Kwankwaso a zaɓe mai zuwa.

Shugaban Matan Kwankwasiyya ta Saudiyyar ta ce duk ‘yan Nijeriya da suke zaune a ƙasashen duniya daban-daban yana da muhimmanci su ma su dawo su karɓi wannan rijistar katin zaɓen, domin lokacin zaɓe su riƙa dawowa su yi zaɓe na mutane masu nagarta da za su kawo gyara a ƙasar nan, musamman jagoransu Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin shugaban kasa.

Hajiya Mariya Ali Zage ta ce tana goyon bayan a samar da doka a kundin tsarin mulki na ƙasar nan da za a sahale wa ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje su riƙa zaɓe a ƙasashen da suke da zama lokacin zaɓe.

Ta ce jagoransu na Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yana da ɗimbin magoya baya a ciki da wajen ƙasar nan, kuma in za a sami damar ‘yan Nijeriya su kaɗa ƙuri’a a ƙasashe da suke zaune zai sami ƙuri’u masu yawa idan aka ce ‘yan Nijeriya mazauna Saudi Arebiya da Dubai da sauran ƙasashen duniya za su yi zaɓe za a san masoyan Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir da suke ƙasashen waje ma suna da yawa sosai.

A ƙarshe, Hajiya Zage ta ƙara da jinjina wa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa irin ayyuka da yake gudanarwa na cigaban al’ummar jihar Kano a fannoni da dama.

  • Related Posts

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?