Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana Alhaji Aminu Ɗantata da Uba ne jagora ne nagari abin koyi.
Barista Isma’il Ahmad, shugaban Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGi),
wanda Mustapha Ali Inda Awa ya yi magana a madadinsa ne ya bayyana hakan a lokacin da suka kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Ya ce sun zo wannan ta’aziyya ne domin nuna alhini na rashin da aka yi a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya na Alhaji Aminu Alasan Ɗantata.
Ya ce suna addu’ar Allah ya gafarta masa, ayyuka da ya yi na alkhari su bi shi ya shigar masa cikin mizaninsa, kuma abin da ya bari Allah ya amfanar da su, su cigaba da irin kyawawan abubuwan da yake na alheri.
Ya ce akwai mu’amaloli masu kyau da ya gudanar a lokacin rayuwarsa, mutum ne da ba ya ƙyamar jama’a, kuma mai taimako a kodayaushe, mai shiga cikin sha’anin al’umma, kuma ya ɗora mutane a kan abubuwa na alkhairi.
Batista Ismail Ahmed ya ce, kullum kiran da marigayi yake a cigaba da ƙoƙarin da riƙe al’umma a taimaka musu, musamman matasa yadda za su taso su zama masu amfani a cikin al’umma.






