Daga Ibrahim Muhammad
An soma gudanar da gasar kacici-kacici ta ‘yan makarantun Kimiyya da Fasaha na jihar Kano ta Abba Gida-Gida da aka ƙaddamar a ɗakin taro na gidan gwamnati a ranar Asabar.
Babban sakataren Hukumar makarantun Kimiyya da Fasaha na jihar Kano, Farfesa Ɗahiru Saleh Muhammad ya ce, zuwan gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, an ƙaddamar da wata doka a kan farfaɗo da ilimi.
Ya ƙara da cewa dokar ta farfaɗo da ilimin Kimiyya da Fasaha da aka yi a jami’ar Bayero, ita ta ba su dama duba mene ne ake yi a ilimin Kimiyya da Fasaha a baya da yanzu ba a yi, sai suka gano ba a yin wasu abubuwan har ma da kacici-kacici irin wannan, shi ne suka dawo da shirya gasar har ma suka ƙara da baje kolin Fasaha na makarantun Fasaha.
Ya ce Hukumar makarantun Kimiyya babu abin da za su ce wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, saboda yana ba da kulawa gare su, wanda shi ya sa suke bijiro da abubuwan inganta ilimin Kimiyya da Fasaha ake ta samun nasara a kai.
Furofesa Ɗahiru Saleh Muhammad Babban Sakataren Hukumar makarantun Kimiyya da Fasaha na Kano ya ce, makarantun Hukumar 49 ne suka shiga cikin gasar, sun kuma rarraba su ne shitya shida. An soma buɗewa da shirya ɗaya ragowar kuma za su biyo baya a mako na gaba, kuma za a je zagaye na biyu har zuwa ƙarshen gasar.
A yayin buɗe gasar kacici kacicin mai bai wa Gwamna shawara a kan Kimiyya da Fasaha, Hon. Habibu El-yakub ya bayyana irin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na ganin ta kyautata harkar ilimi, ta ware wa ilimi kaso mafi tsoka a kasafin kuɗi da kuma tura ɗalibai ƙasashen waje ƙaro ilimi da samar da kayan aiki a makarantun Firamare a dana Sakandire a duk faɗin jihar Kano.
Daga cikin mahalarta taron da aka yi na ƙaddamar da buɗe gasar kacici-kacicin Abba Gida-Gida na makarantun Kimiyya da Fasaha na jihar Kano, akwai babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi na jihar Kano, Alhaji Bashir Baffa, wanda ya wakilci Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Gwani Ali Bukar Makoɗa.






