Daga Ibrahim Muhammad
An amince da N20,000 a matsayin mafi ƙarancin sadakin aure a jihar Kano. Wannan mataki na daga cikin sabbin ƙa’idoji da aka tsara domin sauƙaƙa wa al’umma aiwatar da auren Musulunci cikin sauƙi.
An zartar da hakan ne bayan wani taro da ya haɗa Hukumar Zakka da Hubusi ta Kano da Hukumar Shari’a da Majalisar Malamai da Kungiyar Limaman Juma’a da Ƙungiyar Ma’aikatan Zakka da Waƙafi ta Ƙasa da aka gudanar ranar Alhamis a Kano.
Bayan batun ƙayyade sadakin, an kuma amince da Naira miliyan 150 a matsayin diyya ga wanda aka kashe bisa kuskure, sai kuma Naira 985 a matsayin nisabin Zakka, duka bisa sabbin lissafi da aka yi da darajar kuɗin Dirhami
Farfesa Aliyu Tahiru Muhammad daga Jami’ar Bayero Kano, wanda shi ne Babban Sakataren Ƙungiyar Ma’aikatan Zakka da Waƙafi ta Ƙasa, ya bayyana cewa za a riƙa gudanar da irin wannan taro duk bayan watanni uku, domin duba yiwuwar sabunta waɗannan ƙa’idoji daidai da yanayin tattalin arziƙi.
A ƙarshe, an bayyana niyyar sanar da gwamnatin jihar da kuma shirya wayar da kai ga al’umma, ciki har da amfani da kafafen yaɗa labarai domin isar da saƙo cikin sauƙi da fahimta.






