An Gudanar Da Baje Koli Na Ƙasa Karo Na 11 Kan Sarrafa Abinci Mai Gina Jiki A Kano

Daga Ibrahim Muhammad

An gudanar da baje kolin kayan abinci masu gina jiki na ƙasa karo na sha ɗaya a jihar Kano da wasu cibiyoyin masana a kan harkar noma suka shirya da ya sami halartar masu ruwa da tsaki a harkar noma da sarrafa abinci.

Kwamishinan Lafiya na jihar Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya wakilci Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a yayin taron ya yaba wa masu shirya taron bisa ƙoƙarinsu na ganin an samar da abinci mai gina jiki ga al’umma, ya kuma bayyana irin ayyuka da gwamnatin Kano ke gudanarwa don samar da abinci mai gina jiki musamman ga mata da ƙananan yara.

Shi ma ɗaya daga cikin mahalarta taron, kuma shugaban gamayyar kungiyoyin manoma na ƙasa (AFAN), Dakta Faruk Rabi’u Mudi ya bayyana cewa, noma ne kaɗai ke iya kawar da rashin abinci mai gina jiki da yunwa da fatara da talauci, shi ne kuma ya fi ba da aikin yi a kowane sashe a duniya.

Taron yana ƙarfafa manoma a kan sarrafa abinci, matasa su sami aikin yi, manoma su gane me ma ya kamata su noma da lokacin da ya dace su yi noman da wurin da za su yi.

Ya yi nuni da cewa duk inda ake wata sana’a idan ba riba za a sami rashin jin daɗi, don haka a halin da ake ciki idan taki yana tsada kayan abinci yana sauka ba wanda zai so ya yi noman, dole sai gwamnati ta tallafa wa manoma.

Dakta Faruk Rabi’u Mudi ya ce, kowace ƙasa a duniya gwamnatoci na tallafawa manomansu ba don komai ba kuwa sai saboda ƙasarsu ta zauna lafiya. “Idan babu abinci a wadace, zaman lafiya na iya yin ƙaranci,” in ji shi.

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban sashen Centre for Dry Land Agriculture (CDA), Farfesa Sunusi Gaya ya bayyana cewa Cibiyar tasu za ta cigaba da yin bincike domin zaƙulo abubuwa na Kimiyya da za su taimaka wajen haɓaka noma da samar da abinci mai amfani wajen inganta lafiyar al’umma.

Shi ma a nasa ɓangaren Farfesa Murtala Muhammad Badamasi daga Jami’ar Bayero da ke Kano, wanda kuma Mataimakin Darakta ne na ba da horo na Centre for Dry Land Agriculture ya ce, sun zo domin baje kolin kayan amfanin gona masu gina jiki ne karo na 11. Kowace shekara ana yi, na bana aka yi a jihar Kano da masana na Kimiyya kan baje koli na sabbin fasahohin da aka samar na amfanin gona.

Ya ce irin wannan nake kolin yana da muhimmanci domin hakan na yin tasiri ga inganta harkokin noma. Sannan matasa da manya da magidanta su dama wajen sanin cimakar gina jiki da kuma haɓɓaka basira da ƙwaƙwalwa na yara ƙanana.

Farfesa Murtala ya ce CDA ta yi haɗin gwiwa da Havestplus wajen samar da sababbin fasaha na sinadarin Zink da suka sanya shi a cikin shinkafa wanda a baya babu shi.

Ya yi fatan manoma za su ɗauki sabon irin shinkafar don yada shi ga mutane su noma don ci su amfana don gina jiki domin ba ta da wata matsala.

Shi ma Farfesa Abba Gambo mai bai wa Gwamnoni 36 na ƙasar nan shawara a kan aikin noma da yake zantawa da ‘yan jarida bayan taron ya ce taron muhimmine domin yanzu akwai abinci da ba shi da sinadarai masu kyau na gina jiki don haka yanzu Havestplus abin da suka yi sun saka sinadarai irin na bitamin A da B a cikin abincinmu na gida kamar su sa wa da masara da da shinkafa da aka zo aka yi baje kolin abinci kala-kala masu gina jiki.

Ya ce wannan taron ya nuna ba lallai sai an fita ƙasashen waje ba sannan za mu samar da abincin da zai gina jiki muna da nau’ikan abincinmu iri-iri da muke da su da za su iya samar da sinadarai masu gina jiki.

Ya yi kira ga Gwamnonin ƙasar a kan su ƙara ba da gudunmawa ga manoma musamman na karkara wanda sune suke noma shekara da shekaru su sami taki kan lokaci da ingantaccen irin da sauran kayayyaki kafin damina ta faɗi da damina ta shigo sai su shiga aikin noma ba tare da tsako ba.

Farfesa Abba Gambo ya ce sun bai wa gwamnatoci shawara a kan tsadar taki da ake fama da shi, kuma akwai daga cikin Gwamnonin wani ya raba takin kyauta, wani ya raba kuɗin takin biyu ya saukakawa manoma, akwai Gwamnoni da suka bi manoma na gaske bana ofis har gonakinsu ana ba su taki kuma an ga amfanin hakan.

  • Related Posts

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya damƙa Lambar Karramawa ta Ƙasa a Ayyukan Hidimta wa Al’umma (NEAPS) 2025 ga Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa ayyukan da gwamnati ta gudanar…

    Tsarin Kwankwasiyya Ne Ya Fi Dacewar Da Al’ummar Kano -Injiniya Iliyasu Usman

    Daga Ibrahim Muhammad An bayyana ƙaramar hukumar Nasarawa da ke jihar Kano da cewa suna zaune lafiya babu rigimar siyasa ko wani abu na daban a tsakanin ‘yan Kwankwasiyya, jagorancinsu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?