Daga Ibrahim Muhammad Kano
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na Hukumar yi wa kamfanoni rijista (CAC) a jihar Kano, inda aka tattauna a kan yadda za a kyautata da inganta hulɗa ta fasahar zamani a tsakaninsu da abokan mu’amalarsu.
Taron an gudanar da shi ne ranar Litinin a ƙarƙashin jagorancin shugaban Hukumar na ƙasa, Husaini Ishaq Magaji da mai masaukin baƙi shugabar Hukumar ta jihar Kano, Aisha Dattijo.
Taron ya sami halartar shugaban ƙungiyar lauyoyi reshen Ungogo na jihar Kano, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe da shugabanni da ‘yan kasuwa da masu masana’antu.
A jawabinsa, Hussaini Ishaq Magaji ya ce, taron na Kano shi ne zama na uku makamancinsa da aka yi a ƙasar nan a wasu jihohi daban-daban a cikin wannan shekarar ta 2025 tsakaninsu da abokan hulɗarsu.
Ya ce taron ana yi ne saboda su saurari ƙorafe-ƙorafe na wurare da ya kamata su gyara a gudanar da aikinsu su gyara wanda da ma ya kama a take za a gyara musu a taron saboda sun zo na ƙwararru a ɓangarori daban-daban na Hukumar domin su sauƙaƙa gudanar da kasuwanci cikin sauƙi.
Husaini Ishaq Magaji ya ce, suna da yawan buƙata da ga abokan hulɗar da ya fi ƙarfin ɗan’adam ya yi shi lokaci guda, kamar misali a yau kawai ya duba ya ga masu so a yi musu rijistar kamfani sun kai mutum 7,000 in aka yi la’akari da ma’aikata da suke da su ta yaya za su iya duba su yi bibiyar takardun da miƙo musu na buƙatar har su ba da izinin a yi yau? Gobe masu neman buƙatar za su ninka.
Ya ce saboda haka idan ba sun yi amfani da fasahar zamani ta AI ba, ba za a iya magance al’amuran ba.
“Mun gode wa Allah yanzu muna aiwatar da aiki da fasahar mataki-mataki. Ɓangaren farko shi ne ɓangaren rijistar harkokin kasuwanci da neman suna, kowa yana jin daɗi abokan hulɗarmu yanzu duk wanda zai
rijistar kasuwancinsa a take zai same shi a ƙasa da mintuna 10,” in ji shi.
Ya ce a yanzu duk duniya Hukumar CAC ta ƙasar nan ce ke iya yi wa mutum rijistar kasuwanci a ƙasa da minti 10. “Babu waɗanda suka kai wannan matakin sai mu. Wannan a ɓangare ɗaya ke nan. Muna da ɓangarori na ayyukanmu da muke yi kamar yin rijistar kamfanoni da ƙungiyoyi da sauran abubuwa da za su zo da tsarin tafiya da fasahar zamani domin sauƙaƙa wa al’umma,” ya jaddada.
Hussain Ishaq Magaji ya ce a ƙananan kasuwanci kawai a ƙasar nan daga bara zuwa bana sun yi wa ƙananan kamfanoni sama da miliyan huɗu rijista, mafi yawa masu harkar POS ne, waɗanda aka sauƙaƙa musu babu buƙatar sai sun zo Hukumar ma sannan su yi rijista. Sun kai rijistar ƙarƙashin waɗannan kamfanonin POS ɗin nasu, hakan ta sa adadin masu POS na da yawa.
Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabin sa albarka akwai shugaban ƙungiyar lauyoyi reshen Ungogo na jihar Kano, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe da ya yaba wa irin ƙoƙarin Hukumar wajen ƙoƙarin kawo matakai na sauƙaƙa yin rijista da take ta hanyar shigo da fasahar zamani.
Barista Gwadabe ya ja hankalin mahalarta taron su yi amfani da abubuwan da suka ji don samun sauƙi a hulɗa da Hukumar. Sannan ya yi fatan lauyoyi za su sami ƙarin dama sosai a irin ayyuka da suke gudanarwa da suka shafi hulɗa da Hukumar yi wa kamfanoni na ƙasa rijista.








